Manoma a Kano Za Su Caɓa, an Fara Raba Tirelolin Taki Kyauta Ga Talakawa

Manoma a Kano Za Su Caɓa, an Fara Raba Tirelolin Taki Kyauta Ga Talakawa

  • A yayin da damunar bana ta kankama a Arewa, an fara rabon taki ga manoma a kananan hukumomin jihar Kano
  • Sanata Barau Jibrin ne ya kaddamar da fara rabon takin ga manoma a fadin jihar Kano a jiya Talata, 16 ga watan Yuli
  • Mataimakin shugaban majalisar dokoki ya yi bayani kan yadda rabon zai kasance da kuma yin kira ga manoma

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Mataimakin shugaban majalisar dokokin Najeriya, Sanata Barau Jibrin ya kaddamar da rabon taki a jihar Kano.

Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa za a raba taki har tirela 69 ga manoma a dukkan ƙananan hukumomin da ke jihar.

Kara karanta wannan

Majalisar Kano ta bayyana matsayin Aminu Ado Bayero bayan naɗa sababbin sarakuna 3

Rabon taki
An fara raba taki ga manoma a Kano. Hoto: Barau I. Jibrin
Asali: Facebook

Legit ta gano bayanan da Sanata Barau Jibrin ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka fara raba taki a Kano

Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa ya fara raba takin zamani ga manoma a kananan hukumomin Danbatta da Makoda a jiya.

An ba ƙananan hukumomin buhunan taki 4,100 wanda daga nan kuma za a cigaba da rabon a sauran yankunan jihar Kano.

A yayin rabon, karamar hukumar Danbatta ta samu buhunan taki 2,804 sai kuma karamar hukumar Makoda ta samu buhuna 1,980.

Dalilin raba taki ga manoman Kano

Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa ya raba takin ne domin inganta noma da samar da wadataccen abinci a Najeriya.

Haka zalika Sanatan ya yi kira na musamman ga manoma kan yin amfani da takin ta hanyar da ya dace domin samun amfanin gona yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba ya ɗauki muhimmin mataki na kawo ƙarshen masu ƙwacen waya

Har ila yau, Sanatan ya bayyana cewa zai cigaba da kokari wajen ganin al'umma jihar Kano sun cigaba da shan romon dimokuraɗiyya.

Barau Jibrin ya karbi yan NNPP

A wani rahoton, kun ji cewa a yayin da siyasar Kano ke cigaba da ɗaukan sabon salo, wasu magoya bayan Abba Kabir Yusuf sun sauya sheƙa daga NNPP.

Matasan da suka kasance ƴaƴan jam'iyyar NNPP sun koma tafiyar APC kuma mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karbesu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng