Shugaban APC Abdullahi Ganduje Ya Fadi Dalilin Karuwar Cin Hanci da Rashawa

Shugaban APC Abdullahi Ganduje Ya Fadi Dalilin Karuwar Cin Hanci da Rashawa

  • Shugaban jam'iyya mai mulki na APC, Abdullahi Umar Ganduje ya dora alhakin karuwar cin hanci da rashawa kan INEC
  • Haka kuma ya zargi talakawan kasar nan da ta'azzara cin hanci domin sai an biya su kafin su yi zabe
  • Shugaban, wanda tsohon gwamnan Kano ne da ke fuskantar tuhumar rashawa ya kara da cewa a bar hukumomi su yi aikinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana dalilin da ya sa ake kara samun cin hanci da rashawa a Najeriya. Shugaban, wanda tsohon gwamnan Kano ne ya dora laifin kan gazawar hukumar zabe da sauran Hukumomi da talakawan Najeriya.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba ya ɗauki muhimmin mataki na kawo ƙarshen masu ƙwacen waya

Ganduje
Abdullahi Ganduje ya ce hukumomin yaki da rashawa sun gaza aikinsu Hoto: Sani Gilashi Haruna
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Dakta Ganduje ya ce hukumomin ba su iya yakar cin hanci da rashawa yadda ya kamata, saboda haka lamarin ke ta'azzara.

Me ake bukata domin yakar rashawa?

Tsohon gwamnan na Kano sau biyu, Abdullahi Umar Ganduje ya ce ana bukatar a karfafa wa hukumomi su yi aikinsu domin kakkabe rashawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce idan an ba su dama, hukumomin za su iya gudanar da aikin dakile rashawa ba tare da ganin laifin 'yan siyasa ba, Peoples Gazette ta wallafa.

"Talakawa ba su da gaskiya," Ganduje

Dakta Abdullahi Umar Ganduje, wanda shi ne shugaban APC a yanzu ya ce talakawan Najeriya na ta'azzara cin hanci.

Ya fadi haka ne yayin taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar fa ya gudana a Abuja, inda ya kara da cewa da yawansu ba sa yin zabe sai an biya su.

Kara karanta wannan

"Kotu ta yi adalci," Gwamnatin Abba ta jinjina hukuncin rikicin masarautun Kano

Shugaban, wanda gwamnatin Kano ke tuhuma da rashawa ya kara da cewa dole hukumomi su yi aikinsu idan ana son a samu gyara.

Rashawa: Gwamnatin Kano ta maka Ganduje kotu

A wani labarin kun ji cewa gwamnatin Kano ta sake shigar da shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje kara bisa zargin almundahana. Gwamnatin na zargin Ganduje da handame N24bn da hadin bakin kwamishinansa lokacin ya na gwamnan Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.