Majalisar Kano Ta Bayyana Matsayin Aminu Ado Bayero Bayan Naɗa Sababbin Sarakuna 3

Majalisar Kano Ta Bayyana Matsayin Aminu Ado Bayero Bayan Naɗa Sababbin Sarakuna 3

  • Majalisar dokokin jihar Kano ta yi bayani kan matsayin Sarkin Kano na 15, mai martaba Aminu Ado Bayero bayan naɗa nada sarakuna uku
  • Shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawal Hussain ne ya bayyana haka a jiya Talata bayan tabbatar da sababbin masarautu a jihar
  • Lawal Hussain ta kuma bayyana abin da ake buƙata mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero ya aikata cikin gaggawa bayan sabon hukuncin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Dambarwar sarauta na cigaba da ɗaukan hankula bayan an sake nada sarakuna uku a jihar Kano.

Biyo bayan lamarin, shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar ya bayyana matsayin mai martaba Aminu Ado Bayero.

Kara karanta wannan

Majalisar Kano ta amince da kirkirar masarautu 3 karkashin Sarki Sanusi II

Majalisar Kano
Majalisar Kano ta bukaci Aminu Ado Bayero ya ajiye sarauta. Hoto: Olusegun Adeniya.
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Kano, Lawal Hussain ne ya yi bayanin a jiya Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matsayin Aminu Ado Bayero a Kano

Shugaban masu rinjaye a majalisar jihar Kano, Lawal Hussain ya ce a yanzu haka Aminu Ado Bayero bai kan wata ingantacciyar sarauta.

Lawal Hussain ya fadi haka ne biyo bayan hukuncin da babbar kotun jihar Kano ta yi na tabbatar da Muhammadu Sanusi II a kan karaga.

Saboda haka dan majalisar ya ce ya kamata Aminu Ado ya daina kiran kansa da sarki kuma ya maido da kayan sarauta ga gwamnati.

Dalilin kirkiro masarautu a Kano

Haka zalika dan majalisar ya ce gwamnati na so masarautun jihar Kano su dawo yadda su ke kafin zuwan Abdullahi Umar Ganduje.

Saboda haka ne aka kirkiro da sarakuna uku a Rano, Karaye da Gaya kuma hakan zai dawo da martabar jihar Kano a idon duniya.

Kara karanta wannan

Ana jimamin rasuwar Jagaban, wani ɗan majalisar tarayya daga Kaduna ya mutu

Lawal Hussain ya kuma tabbatar da cewa sababbin sarakunan suna kasa da sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II.

Sarautar Kano: Kotu za ta saurari kara

A wani rahoton, kun ji cewa kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja ta shirya fara sauraron ƙararrakin da ke gabanta kan rikicin masarautar Kano.

Shugabar kotun ɗaukaka ƙara, mai shari'a Monica Dongban-Mensem ta kafa kwamiti mai alƙalai uku da zai saurari ƙararrakin guda huɗu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng