Gwamnan APC Ya Bijirewa Umarnin Kotun Koli, Ya Nada Ciyamomin Rikon Kwarya

Gwamnan APC Ya Bijirewa Umarnin Kotun Koli, Ya Nada Ciyamomin Rikon Kwarya

  • Duk da hukuncin kotun kan nada shugabannin rikon kananan hukumomi, Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya nada kantomomi a Ondo
  • An ruwaito cewa Gwamna Aiyedatiwa ya umurci shugabannin rikon kwarya na kananan hukumomi 18 na jihar da su kama aiki
  • Kayode Ajulo, kwamishinan shari’a na Ondo, ya ce gwamnan ya yi amfani da ‘yancinsa na kundin mulki wajen nada kantomomin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ondo - Lucky Aiyedatiwa, gwamnan Ondo, ya umurci shugabannin rikon kwarya na kananan hukumomi 18 da kansilolin gundumomi 33 na jihar da su kama aiki.

A ranar 11 ga watan Yuli muka ruwaito cewa kotun koli ta amince da rokon gwamnatin tarayya na neman a 'yanta kananan hukumomi daga gwamnatin jihohi.

Kara karanta wannan

Zargin rub da ciki kan N24bn: Gwamnatin Kano ta maka tsohon kwamishina Garo a kotu

Gwamnan Ondo ya yi magana kan nada ciyamomin rikon kwarya
Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya nada shugabannin rikon kwarya. Hoto: @LuckyAiyedatiwa
Asali: Facebook

Kotun ta soki yadda jihohi ke nada ciyamomin rikon kwarya tare da nanata cewa ya kamata a zabi shugabannin kananan hukumomi ta hanyar dimokuradiyya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Ondo ta nada ciyamomin riko

Duk da hukuncin da kotun ta yanke, jaridar The Cable ta ruwaito Gwamna Aiyedatiwa ya umarci kwamitocin rikon kwaryar da su karbi ragamar mulki cikin gaggawa.

A ranar 10 ga Yuli, gwamnatin Ondo ta fitar da jerin sunayen shugabannin rikon kwarya na kananan hukumomi 18 da gundumomi 33.

Aiyedatiwa ya nada kusan mambobi 357 a kwamitocin rikon kwaryar, duk da cewa babbar kotun jihar Ondo ta soke nadin ciyamomi da kansilolin rikon.

Dalilin nada kantomomi a jihar Ondo

Kayode Ajulo, kwamishinan shari’a na Ondo, ya ce gwamnan ya yi amfani da ‘yancinsa na kundin tsarin mulki wajen nada ciyamomi da kansilolin rikon kwarya.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya hango matsaloli a ƴancin kananan hukumomin Najeriya

Shi kuma kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, Amidu Takuro ya ce ba jihar Ondo ce kadai hukuncin kotun koli ya shafa ba.

Amidu Takuro, ya kara da cewa ba za a iya gudanar da zaben kananan hukumomin jihar cikin gaggawa ba, kamar yadda jaridar Tribune ta ruwaito.

Kwamishinonin sun jaddada rawar da kantomomin ke takawa wajen tafiyar da sha'anin mulki yayin da jihar ke shiryawa zabubbukan kananan hukumomi bisa tanadin doka.

Sabon gwamna ya dakatar da ciyamomi

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya amince da dakatar da shugabannin kananan hukumomi 17 domin samun damar gudanar da gamsasshen bincike.

Babban mai taimakawa mai girma gwamna kan harkokin yada labarai, Gyang Bere, shi ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.