Gwamna Abba Ya Nada Sababbin Sarakuna a Masarautun da Ya Kirkiro a Kano

Gwamna Abba Ya Nada Sababbin Sarakuna a Masarautun da Ya Kirkiro a Kano

  • Gwamnan jihar Kano ya naɗa sababbin sarakuna masu daraja ta biyu a masarautun Gaya, Karaye da Rano
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa sarakunan ne biyo bayan rattaɓa hannu da ya yi kan dokar da ta ƙirƙiro masarautun a ranar Talata, 16 ga watan Yulin 2024
  • Sanarwar naɗin wacce mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ta ce naɗin na su zai fara aiki ne nan take

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya amince da naɗin sarakuna masu daraja ta biyu a masarautun Gaya, Karaye da Rano.

Naɗin sarakunan na zuwa ne bayan gwamnan ya rattaɓa hannu kan dokar da ta ƙirƙiro su a ranar Talata, 16 ga watan Yulin 2024.

Kara karanta wannan

Magana ta ƙare, Gwamna Abba Kabir ya kirƙiro sababbin masarautu 3 a jihar Kano

Gwamna Abba ya nada sababbin sarakuna a Kano
Gwamna Abba ya nada sarakuna a masarautun Gaya, Karaye da Rano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya sanya a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Waɗanne sababbin sarakuna aka naɗa?

Sababbin sarakunan sun haɗa da Alhaji Muhamad Maharaz Karaye a matsayin Sarkin Gaya, wanda kafin naɗinsa shi ne Hakimin Rogo.

Alhaji Muhammad Isa Umar a matsayin Sarkin Rano, wanda kafin naɗinsa shi ne Hakimin Bunkure.

Tuɓaɓɓen Sarkin tsohuwar masarautar Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir Gaya, an sake naɗa shi a matsayin Sarkin Gaya.

Saɓanin sauran sarakunan da gwamnan ya tuɓe a kwanakin baya, Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir, ya karɓi ƙaddararsa inda ya nuna shirinsa na yin aiki a kowane muƙami bayan ba da sanarwar tuɓe shi.

Gwamna Abba ya taya sarakuna murna

Gwamnan ya taya sababbin sarakunan murnar naɗin da aka yi musu sannan ya buƙace su da kasance masu kula da al'ada, zaman lafiya da haɗin kan al'umma a masarautunsu.

Kara karanta wannan

Gwamna ya aike da saƙo bayan ɗan majalisar tarayya daga Kaduna ya rasu

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa naɗin na su zai fara aiki ne nan take.

Majalisar Kano ta ƙirƙiro masarautu

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dokokin jihar Kano ta amince da ƙudirin ƙirƙirar sababbin masarautu guda uku masu sarakuna masu daraja ta biyu a jihar.

Masarautun sun haɗa da na Gaya da Karaye da kuma masarautar Rano wadanda duka su na cikin masarautun da aka rushe a watan Mayun 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng