NYSC: Ƴan Bautar Kasa Sun Fara da Kafar Dama, Gwamna Ya Raba Masu Kyautar N26m
- Gwamna Ahmed Usman Ododo ya bai wa matasa ƴan bautar ƙasa da aka tura jihar Kogi kyautar kudi sama da N26m
- Hakan na nufin kowane matashi daga cikin 1,326 da suka halarci sansanin horarwa na NYSC a Asaya zai samu N20,000 daga gwamnatin Kogi
- Da yake jawabi a wurin taron rufe horar da ƴan rukunin B kashi na 1, Gwamna Ododo ya ce tallafin zai kara zaburar da matasan a wuraren aikinsu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kogi - Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Ahmed Ododo, ya bayar da kyautar kuɗi sama da Naira miliyan 26 ga ‘yan bautar kasa (NYSC) da aka tura jihar.
Hakan na nufin matasan masu yiwa ƙasa hudima 1,326 da aka tura Kogi za su samu kyautar N20,000 kowanensu daga Gwamna Ahmed Ododo.
Gwamnan ya rabawa ƴan bautar ƙasa waɗannan kuɗaɗe ne a wurin taron rufe horar da ƴan rukunin B kashi na 1 a sansanin NYSC da ke Asaya a jihar Kogi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ahmed Ododo ya samu wakilcin mataimakinsa, Joel Salifu Oyibo a wurin taron wanda ya gudana ranar Talata, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.
Gwamma Ododo zai karrama ƴan NYSC
Da yake jawabi, Gwamnan ya ce an ba su wannan tallafi ne domin zaburar da su, su yi aiki tuƙuru a wuraren da za a tura su aiki.
Ya ƙara da cewa gwamnatin Kogi za ta karrama jajirtattun ƴan bautar ƙasa bayan sun kammala aikinsu na tsawon watanni 12, rahoton The Cable.
Gwamna Ododo ya tabbatarwa da ‘yan NYSC cewa gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a guiwa ba wajen tabbatar da tsaro da walwalar su a tsawon lokacin da za su shafe a Kogi.
Da yake ayyana rufe horar da matasan rukunin B kashi na 1, Gwamnan ya jaddada kudirin gwamnatinsa na inganta sansanin NYSC da ke Asaya.
Abubakar Sanusi, wani matashi ɗan bautar kasa da aka tura Kogi ya tabbatar da haka ga wakilin Legit Hausa.
Matashin ya shaida mana cewa mataimakin gwamna ne ya wakilci Gwamna a taron rufewa kuma ya masu alkawarin za su samu tsaro idan suka zauna a Kogi.
"Eh tabbas an ce za a bamu N20,000 amma na ji wasu na raɗe-raɗin ban da waɗanda suka nemi canjin jihar da za su yi aiki," in ji shi.
Gwamnan Abia ya ware N45,000 ga ma'aikata
A wani rahoton na daban Gwamnatin jihar Abia ta amince da biyan ma'aikatan jihar N15,000 tsawon watanni uku wanda zai kama N45,000 domin rage musu radadi.
Hakan na cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai a jihar, Prince Okey Kanu ya fitar a jiya Litinin 15 ga watan Yulin 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng