Kotun Daukaka Kara Ta Yi Hukunci Kan Karar Neman Tsige Gwamnan APC
- Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta yi hukunci kan ƙarar da ke ƙalubalantar nasarar Hope Uzodinma a zaɓen gwamnan jihar Imo
- Kotun ta tabbatar da nasarar da gwamnan ya samu a zaɓen da aka gudanar a ranar, 11 ga watan Nuwamban 2023
- Kotun ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar da jami'iyyun PDP, LP da APM suka shigar inda su ke ƙalubalantar nasarar da Gwamna Hope Uzodinma ya samu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja, ta tabbatar da nasarar Gwamna Hope Uzodinma na jam'iyyar APC, a matsayin gwamnan jihar Imo.
Kotun ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyar PDP da ɗan takararta na gwamna Samuel Anyawu suka shigar su na ƙalubalantar hukuncin kotun zaɓe kan tabbatar da zaɓen Hope Uzodinma a matsayin gwamnan jihar.
Gwamna Hope Uzodinma ya yi nasara a kotu
Kotun ta ce ƙarar ba ta cancanta ba bayan warware duk wasu batutuwan da masu shigar da ƙarar suka gabatar a gabanta, cewar rahoton tashar Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakazalika, kotun ɗaukaka ƙarar ta kuma yi watsi da ɗaukaka ƙarar da jam’iyyar LP da ɗan takararta, Achonu Nneji, da jam'iyyar APM suka yi saboda ba su cancanta ba.
An yi karar Gwamna bayan zaben Imo
Waɗanda suka shigar da ƙarar da ba su gamsu da hukuncin kotun zaɓen ba, sun tunkari kotun ɗaukaka kara ne bisa cewa zaɓen da aka yi a ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023 bai cancanta ba saboda rashin bin dokar zaɓe.
Masu shigar da ƙarar sun kuma ƙalubalanci takardun karatun Hope Uzodimma tare da zargin cewa satifiket ɗinsa na shaidar kammala karatun WAEC, na jabu ne.
Wane hukunci kotun ta yanke?
A yayin da take yanke hukunci, kotun ɗaukaka ƙarar ta bayyana cewa waɗanda suka shigar da ƙarar sun kasa tabbatar da zargin rashin bin dokar zaɓe.
Kotun mai alƙalai uku ƙarƙashin mai shari'a Bitrus Sanga ta kuma bayyana cewa waɗanda suka shigar da ƙara sun gaza tabbatar da cewa gwamnan ya ba hukumar INEC satifiket na jabu.
An dakatar da ƴan majalisu a Imo
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dokokin jihar Imo ta dakatar da ƴan majalisa huɗu bisa zargin suna yunƙurin tsige shugaban majalisar, Chike Olemgbe.
Kakakin majalisar Honorabul Olemgbe ne ya sanar da ɗaukar wannan matakin a zaman ranar Talata, 2 ga watan Yuli, 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng