AYCF: Ƙungiya Ta Fadi Hanyoyin da Matasa Za Su Bi Wajen Yin Zanga Zanga Lafiya

AYCF: Ƙungiya Ta Fadi Hanyoyin da Matasa Za Su Bi Wajen Yin Zanga Zanga Lafiya

  • Kungiyar Arewa Youth Consultative Forum (AYCF) ta yi kira na musamman ga matasa da ke shirin fita zanga zanga a Najeriya
  • Kungiyar ta ba matasan shawara kan yadda ya kamata zanga zangar ta kasance domin kaucewa barkewar rikici a Najeriya
  • Legit ta tattauna da malamin addini, Muhammad Abubakar a jihar Taraba domin jin kiran da zai yi ga matasa kan zanga zanga

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Kungiyar Arewa Youth Consultative Forum (AYCF) ta yi kira ga matasa masu shirin yin zanga zanga a Najeriya.

Kungiyar AYCF ta bukaci matasa su yi amfani da hankali wajen gudanar da zanga zangar domin cimma burinsu cikin sauki.

Kara karanta wannan

Ana shirin zanga zanga, NLC ta turawa majalisa gargadin tsaida ayyuka cak na kwanaki 30

Matasan Najeriya
An bukaci matsa su bi sannu sannu yayin zanga zanga. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyar ta kuma yi kira na musamman ga gwamnatin tarayya wajen kawo saukin rayuwa a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ya kamata ayi zanga zanga

Shugaban kungiyar AYCF, Shettima Yerima ya buƙaci masu zanga zanga da su kaucewa tayar da tarzoma.

Shettima ya ce akwai alamun cewa matasan sun fusata saboda tsananin rayuwa amma duk da haka akwai buƙatar kai zuciya nesa.

Abubuwan da suka fusata matasa

Shugaban kungiyar AYCF ya ce a halin yanzu mafi yawancin matasa ba su da alkibila saboda matsaloli da dama, rahoton the Whistler.

Ya ce akwai matsalolin rashin sana'o'i, talauci da rashin abubuwan more rayuwa da sauransu da suka dabaibaye matasa.

AYCF: 'Ku kai zuciya nesa'

Amma duk da haka ya ce ya kamata matasan su kai zuciya nesa musamman idan za a samu hanyar kawo sauki da ba ta zanga zanga ba.

Kara karanta wannan

Sheikh Kabiru Gombe ya yi magana kan zanga zangar da matasa ke shirin yi a Najeriya

Haka zalika Shettima ya bukaci gwamnatin tarayya da ta dauki matakin gaggawa wajen biyan bukatun matasan domin kaucewa ballewarsu daga burki.

Legit ta tattauna da malamin addini

Legit ta tattauna da malamin addini a kan lamarin inda ya bayyana cewa duk da cewa zanga zanga ta halasata a dokar kasa ya kamata matasa su yi taka tsan tsan.

Malamin ya ce akwai bukatar matasa su san dalilin da ya fitar da su domin dawowa gida daga zarar bukatunsu sun cika.

Ya kuma kara da cewa ya kamata a nisanta zanga zangar da harkokin addini da kungiyar siyasa da sace sace.

APC ta yi magana kan zanga zanga

A wani rahoton, kun ji cewa matasan Najeriya na cigaba da shirye shiryen fara zanga zanga domin kawo karshen tsadar rayuwa da ake fama da ita.

Jam'iyyar APC mai mulki ta yi kira na musamman ga daukacin matasan Najeriya kan dakatar da shirye-shiryen gudanar da zanga zangar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng