NYSC: Matasa Sun Barke da Murna Bayan Gwamna Ya Gwangwaje Kowa da N100,000

NYSC: Matasa Sun Barke da Murna Bayan Gwamna Ya Gwangwaje Kowa da N100,000

  • Matasa masu bautar ƙasa a jihar Lagos sun barke da murna bayan gwamnan jihar ya gwangwaje su da abin alheri
  • Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ba kowane matashi da ya kammala horaswa a yau Talata 16 ga watan Yulin 2024 a jihar N100,000
  • Gwamnan ya kuma ware N5bn domin sake gina sabon sansanin horas da matasan masu bautar ƙasa na din-din-din a jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Lagos ya gwangwaje masu bautar ƙasa da babbar kyauta

Gwamnan ya ba kowane matashi da aka tura bautar ƙasa a jihar N100,000 wanda akalla sun fi 4,000.

Kara karanta wannan

Uba Sani ya ba da umarnin a zane Dan Bilki Kwamanda? Gwamnatin Kaduna ta magantu

Gwamna ya ba matasa masu bautar ƙasa kyautar N100,000
Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Lagos ya ba matasa masu bautar ƙasa kyautar N100,000 . Hoto: Babajide Sanwo-Olu.
Asali: Twitter

NYSC: Sanwo-Olu ya ba matasa N100,000

Sanwo-Olu ya bayyana haka yayin taron kammala horaswa da matasan suka yi na makwanni uku, kamar yadda hadiminta, Jubril Gawat ya wallafa a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan wanda ya sanya kayan bautar kasa ya godewa matasan inda ya dauki hotunan da su domin kara musu karfin guiwa.

Har ila yau, Sanwo-Olu ya amince da ware N5bn domin gina sabon sansanin ƴan bautar ƙasa na din-din-din a jihar.

Ya ce matasa masu bautar ƙasa guda 1000 da suka yi fice za su samu aiki da gwamnatin jihar da za-ran sun kammala bautar ƙasa.

"Duk wani matashi da zai kammala horarsa a yau zai samu N100,000 wanda za a tura masa cikin asusun bankunansa."
"Matasa 100 da suka yi fice a cikin saura za su samu aiki da gwamnatin jihar Lagos bayan kammala bautar ƙasa."

Kara karanta wannan

An kama ɗan Gwamna Zulum da zargin hallaka wani a gidan Gala a Indiya? Gaskiya ta fito

- Babajide Sanwo-Olu

Gwamna Sanwo-Olu ya gwangwaje NYSC da kyauta

Sanwo-Olu ya kuma ba sansanin horas da matasan mota kirar bas domin taimakawa wurin gudanar da ayyukansu.

Wannan alkawuran na gwamnan ya bar matasan cikin farin ciki inda suke ta tattauna lamarin bayan kammala taron.

Legit Hausa ta tattauna da wani ma'aikaci a sansanin horas da matasa a Gombe domin sanin halin da ake ciki.

Umar Faruk ya ce a Gombe babu wani alkawari daga gwamnan jihar kan ba matasan wani kyauta.

"Kamar yadda muka ji a Lagos da Kogi matasan sun damu kyaututtuka ba mu saka rai daman za su samu a nan Gombe ko kadan."

- Umar Faruk

Gwamna Sanwo-Olu ya shawarci ƴan fansho

Kun ji cewa Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ya shawarci ƴan fansho da suka samu kudinsu a jihar kan yadda za su kashe su.

Sanwo-Olu ya ce bai kamata su je su bayar da kudinsu ga taimakon masallaci ko coci ba inda ya ce guminsu ne don haka su kashe yadda suke so.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.