Gwamna Ya Kafa Kwamiti Domin Duba Yiwuwar Aiki da Dokar Kananan Hukumomi
- Gwamna jihar Oyo ya nuna rashin gamsuwa da hukuncin da kotun tarayya ta yi kan yancin ƙananan hukumomi a Najeriya
- Biyo bayan haka, gwamna Seyi Makinde ya tara masu ruwa da tsaki a jihar Oyo domin daukan mataki na gaba kan hukuncin kotun
- A karshen tattaunawar da gwamnan ya yi, ya kafa kwamiti da zai yi nazari kan hukuncin da kotun ta yi domin daukan mataki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya yi taron gaggawa domin duba hukuncin da kotun tarayya ta yi kan yancin ƙananan hukumomi.
Gwamna Seyi Makinde ya yi taron ne domin nuna shakku kan hukuncin da kotun ta yanke a makon da ya wuce.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa cikin waɗanda suka halarci taron akwai kungiyoyin kwadago na jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin taron da Makinde ya kira
Gwamna Seyi Makinde ya bayyana cewa ya kira taron ne domin kore shakku da ruɗani da ya biyo bayan hukuncin kotun tarayya kan kananan hukumomi.
Seyi Makinde ya ce akwai abubuwan da ba su fahimta ba dangane da hukuncin kuma dole a fayyace komai domin kaucewa kuskure.
Kananan hukumomi: Gwamna ya kafa kwamiti
Gwamna Seyi Makinde ya kafa kwamiti domin ya yi nazari kan hukuncin da kotun tarayya ta yanke, rahoton Channels Television.
Kwamitin zai yi kokarin fahimtar hukuncin da kotun ta yanke da kuma duba yiwuwar aiwatar da dokar ba ƙananan hukumomi yanci a jihar Oyo.
Yaushe kwamiti zai gama aiki?
Kwamishinan shari'a na jihar Oyo, Barista Abiodun Aikimo ya ce an ba su makonni shida domin kammala aikin.
A ƙarshe, gwamna Seyi Makinde ya ce za su gudanar da zaben kananan hukumomi nan ba da jimawa ba a jihar Oyo.
Adamawa: An yi zaben kananan hukumomi
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar zabe a Adamawa ta tabbatar da cewa jam'iyyar PDP mai mulki jihar Adamawa ta lashe dukkan kujeru 21 na kananan hukumomi a jihar.
Shugaba hukumar a jihar, Mohammed Umar shi ya tabbatar da haka inda ya ce NNPP ta yi nasara a kujera daya ta kansila a jihar.
Asali: Legit.ng