Majalisar Kano Ta Amince da Kirkirar Masarautu 3 Karkashin Sarki Sanusi II
- Kwana daya bayan yanke hukunci kan rigimar sarautar Kano, Majalisar jihar ya fara shirin kirkirar sababbin masarautu
- Majalisar ta gabatar da kudirin samar da sarakuna guda uku masu girman daraja ta biyu a yau Talata 16 ga watan Yulin 2024
- Masarautun guda uku sun hada da na Rano da Gaya da kuma Karaye da za su kasance ƙarƙashin Sarki Muhammadu Sanusi II
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Majalisar jihar Kano ta gabatar da kudirin kirkirar sababbin masarautu guda uku a jihar.
Kudirin kirkirar sababbin sarakunan masu daraja ta biyu ya tsallake karatu na uku a Majalisar a jihar.
Kano: Majalisar za ta kirkiri masarautu 3
Hadimin Gwamna Abba Kabir a bangaren sadarwar zamani, Hassan Sani Tukur shi ya tabbatar da haka a shafinsa na X a yau Talata 16 ha watan Yulin 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hassan Tukur ya ce masarautun sun hada da na Gaya da Karaye da kuma masarautar Rano wadanda duka suna cikin masarautun da aka rushe a watan Mayun 2024.
Ya ce tuni kudirin ya tsallake karatu na uku wanda idan aka sanyawa hannu sarakunan za su yi aiki karkashin Sarki Muhammadu Sanusi II.
Hakan na nufin an dawo da masarautun da aka rusa a watan Mayun 2024 amma babu labarin na Wudil da Bichi.
Kotu ta yanke hukunci kan rigimar masarautu
Wannan mataki na zuwa ne kwana ɗaya bayan hukuncin da Kotun jihar ta yi kan rigimar masarautu da ake ciki.
Kotun da umarci Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna hudu su bar kiran kansu a matsayin sarakai a jihar.
Dan Agundi ya magantu kan sarautar Kano
A wani labarin, kun ji cewa Sarkin Dawaki Babba, Aminu Dan Agundi ya yi martani kan rigimar sarautar Kano da ake ciki.
Dan Agundi ya ce tun farko akwai babban kuskure wurin mayar da Muhammadu Sanusi II kan kujerar sarauta.
Dan Agundi ya ce Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero shi ne ya cancanci kujerar saboda gadonta ake yi ba zabe ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng