Sheikh Kabiru Gombe Ya Yi Magana Kan Zanga Zangar da Matasa Ke Shirin Yi a Najeriya
- Sakataren ƙungiyar Izala, Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe ya yi magana kan zanga-zangar da matasa ke shiryawa
- Shehin Malamin ya yi kira ga matasa su rungumi zaman lafiya kana su guji duk wani abu da zai iya haifar da tashin hankali
- Sheikh Kabiru Gombe ya bayyana cewa manyan addinai Musulunci da Kiristanci sun koyar da bin hanyar lalama wajen warware kowace irin matsala
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Fitaccen malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe ya yi kira ga matasan Najeriya su rungumi zaman lafiya, su gujewa zanga-zanga.
Sheikh Kabiru Gombe, sakataren kungiyar addinin Musuluncin da aka fi sani da Izala ya shawarci matasa su ƙauracewa zanga-zangar da su ke shiryawa kan yunwa da rashin tsaro.
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Shehin malamin ya jaddada muhimmancin tattaunawar sulhu da bin hanyoyin maslaha wajen warware kowane irin rikici.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kalaman malamin na zuwa ne a daidai lokacin da matasa ke shirya zanga-zanga domin jawo hankalin gwamnati kan halin ƙuncin rayuwa da ake ciki.
Malamin ya roƙi matasa su guji duk wani abu da ka iya haifar da tashin hankali da hargitsi a cikin al'umma.
Kabiru Gombe ya ba matasa shawara
Sheikh Kabir Gombe ya ce:
"Wasu mutane na amfani a kafafen sada zumunta wajen haɗa kan ƴan Najeriya musamman matasa domin su fita zanga-zanga kan yunwa, cire tallafi, ƙarin kuɗin wuta da matsalar tsaro."
Da yake bayyana matsayar addinai kan wannan batu, Malamin ya ce Alkur'ani da Bayibul sun koyar da warware kowane kalubale da ya taso cikin lumana.
"Alkur'ani mai girma da Littafin Injila (Bible) duk sun koyar da zaman lafiya ba hargitsi ba," in ji shi.
Malamin ya roki matasa su zama masu ɗa'a a lokutan wahala.
Malami ya musanta karɓar N16m daga Tinubu
A wani rahoton kun ji cewa Shehin malami, Barista Ishaq Adam Ishaq ya musanta labarin cewa malamai sun karbi kudi har Naira Miliyan 16 daga Bola Ahmed Tinubu.
A wani bidiyon malamin, an jiyo shi ya na cewa babu yadda za a yi shugaban kasa da ya rika tura wa wani kudi kai tsaye kamar yadda ake yayata wa.
Asali: Legit.ng