Majalisar Tarayya ta Gano Yadda Najeriya ke Asarar Biliyoyin Daloli a Duk Shekara

Majalisar Tarayya ta Gano Yadda Najeriya ke Asarar Biliyoyin Daloli a Duk Shekara

  • Majalisar wakilai ta bayyana takaici kan yadda kasar nan ke tafka asara kan hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba
  • Shugaban kwamitin ma'adanai, Jonathan Gbefwi ya ce ana asarar akalla $9bn duk shekara, wanda hakan ba karamar asara ba ce
  • Hon. Gbefwi na ganin lokaci ya yi da ya kamata a dauki matakin kawo karshen hakar ma'adanai da wasu ke yi ba bisa ka'ida ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. FCT, Abuja - Kwamitin majalisar wakilai kan ma'adanai ya bayyana cewa kasar nan na tafka asarar biliyoyi a bangaren ma'adanai duk shekara. Kwamitin ya gano cewa Najeriya na tafka asarar $9bn a duk shekara saboda ayyukan masu hakar ma'adanai ta barauniyar hanya.

Kara karanta wannan

"Hana makiyaya kiwo a sake zai jawo manyan matsaloli 3 a ƙasa," KACRAN

Representatives
Najeriya na asarar $9bn ga hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba Hoto: House of Representative, Federal Republic of Nigeria/Issouf Sanogo
Asali: Facebook

Jaridar The Cable ta wallafa cewa shugaban kwamitin, Jonathan Gbefwi ne ya bayyana haka a ranar Litinin

Majalisa ta bayyana illar hakar ma'adanai

Shugaban kwamitin majalisa kan ma'adanai, Jonathan Gbefwi ya ce hakar ma'adanai da wasu ke yi ba bisa ka'ida ba na jefa kasar cikin hadari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya shaidawa majalisa cewa lokaci ya yi da za a dauki bangaren ma'adanai da muhimmancin gaske domin a mori albarkar da ke sashen.

The Sun ta wallafa cewa dan majalisar ya bayyana damuwa matuka kan yadda kudin kasar nan ke zurarewa saboda ayyukan masu sojan gona.

"Hakar ma'adanai ya jawo rashin tsaro" - Majalisa

Dan majalisar tarayyar ya bayyana damuwa kan yadda hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba ke jawo rashin tsaro a kasa.

Ya ce daga sabani tsakanin masu hakar ma'adanan abin ya ke girma zuwa tashe-tashen hankula a wuraren da ake aikin.

Kara karanta wannan

Zargin N33bn: Bayan kwana 1 a kurkuku, kotu ta ɗauki mataki kan Ministan Buhari

"Hakar ma'adanai ne silar tashin hankali," Abbas

A baya mun ruwaito cewa kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajuddeen ya bayyana yadda hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba ke jawo rashin tsaro.

Rt. Hon. Abbas Tajuddeen ya ce dole ne a tashi tsaye wajen daukar matakan kakkabe hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba a kasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.