Zanga Zanga: Matasan Arewa Sun Yi Gargadi, Sun Fadi Makarkashiyar da Ake Shiryawa
- Yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zanga-zanga, kungiyar matasa a Arewa ta yi gargadi kan haka
- Kungiyar mai suna Arewa Youth Federation ta barranta kanta ta zanga-zangar inda ta ce ana ƙoƙarin mayar da Najeriya baya
- Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Kabir Mutazu ya fitar inda ya gargadi matasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Wata kungiyar matasa a Arewacin Najeriya ta bayyana matsayarta kan shirye-shiryen zanga-zanga.
Kungiyar mai suna Arewa Youth Federation (AYF) ta barranta kanta da zanga-zanga kan gwamnatin Bola Tinubu.
Zanga-zanga: Kungiyar matasan Arewa ta yi gargadi
Shugaban kungiyar, Kabir Mutazu ya tabbatar da haka inda ya ce duka rassan kungiyar a jihohin Arewa ba za su shiga zanga-zangar ba a cewar Daily Nigerian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matazu ya ce mafi yawan masu zanga-zangar suna da wani nufi na mugunta ga kasar domin kawo tashin hankali, Pulse ta tattaro.
"Kungiyar ƴan Arewa ta fahimci yanayin yadda ƙasar ke ciki kuma masu zanga-zangar sun rasa tsari a shirinsu."
"Gudanar da zanga-zanga a wannan hali zai kara rusa ci gaban da aka samu a kasar wanda aka sha wahala wurin samar da shi."
"Arewa Youth Federation ba ta goyon bayan zanga-zangar inda take tare dari bisa dari da gwamnatin Bola Tinubu domin shawo kan matsalolin yankin."
- Kabir Mutazu
Kungiyar AYF ta shawarci Arewa kan zanga-zanga
Kungiyar ta bukaci ƴan Najeriya da su yi fatali da kiran zanga-zangar inda ta ce akwai makarkashiya a ciki.
Ta ce wasu ne marasa kishin kasa ke neman kawo rigima da tarwatsa ci gaban da aka dade ana nema.
Kungiyar AYA ta kori shugaba kan zanga-zanga
Kun ji cewa Kungiyar matasan ta Arewa Youth Ambassadors (AYA) to kori shugabanta, Yahaya Abdullahi kan zanga-zanga.
Kungiyar ta ce ta dauki matakin korar tsohon shugaban ne bisa zargin tattaro kawunan matasa domin zanga-zangar.
AYA ta nemi a binciki tsohon shugabanta, Yahaya Abdullahi da laifin cin hanci wurin shirya zanga-zanga.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng