Hana Zanga Zanga: Malamai Sun Gana da Tinubu, an Gano Duka Abubuwa 3 da Aka Tattauna

Hana Zanga Zanga: Malamai Sun Gana da Tinubu, an Gano Duka Abubuwa 3 da Aka Tattauna

  • Al'ummar Najeriya da dama sun zargi malaman addinin Musulunci da ganawa da gwamnati domin hana zanga zanga
  • Hakan kuma ya biyo bayan ganin hotunan malamai da aka yi tare da Malam Nuhu Ribadu ne a Abuja a makon da ya wuce
  • Sai dai wani malami, Dakta Aliyu Muhammad Sani ya bayyana abin da suka tattauna yayin da suka gana da gwamnatin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A makon da ya wuce ne aka rika yaɗa hotunan wasu malaman addinin Muslunci a fadar shugaban kasa ana zarginsu da karbar kuɗi.

Wasu daga cikin al'umma sun zargi malaman da karbar kudi daga gwamnatin tarayya domin hana zanga zanga da ake shirin yi.

Kara karanta wannan

Ruwa ya ruguza gidaje da rumbunan abinci a Arewa, mutane sun shiga tasko

Malaman Arewa
An gano abin da malamai suka tattauna da Bola Tinubu. Hoto: Abdulrahman Idris Yakubu
Asali: Facebook

Sai dai Dakta Aliyu Muhammad Sani ya bayyana abubuwa uku da ya kai malamai wajen ganawa da gwamnati kamar yadda ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ya kai malamai wajen gwamanti?

1. Taɓarɓarewar tsaro a Najeriya

Malamin addinin Musulunci, dakta Aliyu Muhammad Sani ya ce daga cikin abin da malamai suka tattauna da gwamnati akwai maganar samar da tsaro.

Ya kuma tabbatar da cewa sun gana da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu domin neman mafita.

2. Hauhawar farashin kayan abinci

Dakta Aliyu Muhammad Sani ya kara da cewa sun tattauna kan yadda kayan abinci suke kara tsada a Najeriya.

Ya bayyana cewa malaman sun kuma zauna da ministan da abin ya shafa domin ganin an dauki matakin gaggawa.

3. Magana kan yarjejeniyar Samoa

Har ila yau, Dakta Aliyu Muhammad Sani ya bayyana cewa sun tunkari gwamnati domin tattaunawa kan yarjejeniyar Samoa.

Kara karanta wannan

Shehin malami ya musanta karbar N16m daga Tinubu, ya fadi dalilin ziyartar shugaban kasa

Ya ce waɗannan ne abubuwan da malaman suka nemi gwamantin domin tattaunawa amma aka juya lamarin ga wani abu daban.

Malami ya fadi dalilin zaben Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa a yayin da al'ummar Najeriya ke cigaba da kokawa kan mulkin Bola Tinubu malamin Izala ya bayyana dalilan zaben shi a 2023.

Shugaban majalisar malaman kungiyar Izala, Dakta Ibrahim Jalo Jalingo ne ya bayyana dalilan zaben Tinubu da Kashim Shettima, ya ce ba su nadama.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng