Kungiyar Arewa ta Fatattaki Shugabanta Saboda Goyon Bayan Shirya Zanga Zanga

Kungiyar Arewa ta Fatattaki Shugabanta Saboda Goyon Bayan Shirya Zanga Zanga

  • Wata kungiya mai suna Arewa Youth Ambassadors ta kori shugabanta, Yahaya Abdullahi bisa kiran matasa zanga zanga
  • Kungiyar ta AYA ta yanke hukuncin ne biyo bayan taron gaggawa da su ka yi a Jigawa bayan samun labarin sauya hotunan ofis
  • Yanzu haka an maye gurbin Yahaya Abdullahi da Muhammad Lawal sannan an nemi a binciki tsohon shugaban da cin hanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Kaduna - Kungiyar matasan Arewa ta Arewa Youth Ambassadors (AYA) to kori shugabanta, Yahaya Abdullahi. Kungiyar ta ce an dauki matakin korar tsohon shugaban ne bisa zargin tattaro kawunan matasa domin zanga-zangar kin amincewa da halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

"Muhimman cigaba 3 da za a gani bayan samun 'yanci" Inji Tsohon shugaban karamar hukuma

Bola Tinubu
Kungiyar Arewa ta kori shugabanta saboda amincewa da zanga-zanga Hoto: Asiwaju Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa an maye gurbin Yahaya Abdullahi da Muhammad Lawal.

AYA ta nemi a binciki tsohon shugabanta

Kungiyar matasan Arewa ta AYA ta nemi a binciki tsohon shugabanta, Yahaya Abdullahi da laifin cin hanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ta dauki matakin ne bisa zargin tsohon shugaban da goyon bayan zanga-zanga kan gwamnatin Bola Tinubu.

Nigerian Tribune ta wallafa cewa shugaban ya hori matasa su fito a yi gwagwarmayar zanga-zanga da su.

An tuhumi Yahaya Abdullahi da kabilanci

A taron gaggawa da kungiyar ta gudanar a jihar Jigawa, an zargi Yahaya Abdullahi da kabilanci.

Daya daga cikin kusoshin kungiyar, Namadi Duniya ya ce Yahaya Abdullahi bai nemi a yi zanga-zanga a lokacin Muhammadu Buhari ba saboda dan Arewa ne.

AYA za ta yi taron matasa

Kungiyar matasan Arewa ta AYA ta ce za ta wayar da kan matasa saboda su san muhimmancinsu a shugabanci

Kara karanta wannan

Shehin malami ya musanta karbar N16m daga Tinubu, ya fadi dalilin ziyartar shugaban kasa

Kungiyar na wannan batu bayan ta kori shugabanta Yahaya Abdullahi, inda ta ce akwai bukatar matasa su san kansu.

Zanga-zanga: Sheikh Gumi karfafawa matasa

A wani labarin kun ji cewa malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya ce ba laifi ba ne idan an gudanar da zanga-zanga.

Ya ce zanga zanga ba haramun ba ce, domin ko a baya shugabannin kasar nan sun jagoranci zanga-zanga kuma an wanye kalau.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.