A Ƙarshe, Bola Tinubu Zai Miƙa Sabon Mafi Ƙarancin Albashin Ma'aikata ga Majalisa

A Ƙarshe, Bola Tinubu Zai Miƙa Sabon Mafi Ƙarancin Albashin Ma'aikata ga Majalisa

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ka iya miƙa kudirin sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata ga majalisar tarayya a makon gobe
  • Ministan yaɗa labarai da wayar da kan al'umma, Muhammed Idris ne ya faɗi haka a Abuja, ya ce Tinubu zai gana da ƴan kwadago ranar Alhamis
  • Wannan na zuwa ne bayan kwamitin da aka kara ya miƙa rahotonsa ga Bola Tinubu duk da ƴan kwadago sun kafe a kan N250,000

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Idan komai ya tafi yadda aka tsara, da yiwuwar Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai miƙa ƙudirin sabon mafi ƙarancin albashi ga majalisar tarayya a makon gobe.

Sai dai ana tsammanin Bola Tinubu zai miƙa kudirin ga majalisar tarayya ne bayan ya gana da ƴan kwadago ranar Alhamis mai zuwa.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu, ya faɗi mafita a Najeriya

Bola Tinubu.
Shugaba Tinubu zai gana da ƴan kwadago kan sabon mafi karancin albashi Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Idan dai ba ku manta ba, shugaba Tinubu ya gana da shugabannin kungiyoyin kwadago a ranar Alhamis din makon jiya kan batun mafi karancin albashi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Vanguard ta tatataro cewa kwamitin ƙarin albashi ya riga da ya miƙa rahotonsa ga shugaban ƙasa bayan kammala tattaunawa.

Kwamiti ya miƙa rahoto ga Bola Tinubu

Kwamitin ya miƙa adadi guda biyu sakamakon sabanin da aka samu tsakanin ɓangaren gwamnati da ƴan kwadago.

Yayin da tawagar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu suka yi tayin N62,000, kungiyoyin kwadagon sun bukaci N250,000 a matsayin mafi karancin albashi.

Bayan karɓan rahoton kwamitin, Shugaba Tinubu ya yi alkawarin ganawa da masu ruwa da tsaki domin daidaita adadin kafin mika kudirin dokar ga majalisa.

Shugaba Bola Tinubu zai gana da NLC

Da yake zantawa da manema labarai bayan taron majalisar zartaswa (FEC) yau Litinin, ministan yaɗa labarai Muhammed Idiris ya ce Tinubu zai gana da ƴan kwadago.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya ji koken ƴan Najeriya, ya bada rallafin tirelolin shinkafa a jihohi 36

Ministan ya bayyana cewa Bola Tinubu zai miƙa kudirin sabon mafi ƙarancin albashi ga majalisar tarayya bayan ya gana da ƴan kwadago ranar Alhamis.

Har ila yau Muhammed Idris ya ce majalisar zartaswa za ta aika da abin da ya bayyana a matsayin gyara ga kasafin kudin 2024 ga majalisar dokokin kasar, Daily Trust ta ruwaito.

Tinubu ya jagoranci taron FEC

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu na jagorantar taron majalisar zartaswa ta tarayya a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ranar Litinin, 15 ga watan Yuli.

Kafin fara taron majalisar ta yi shiru na tsawon minti ɗaya domin girmama marigayi Ahmed Muhammed Gusau wanda ya rasu a watan Mayu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262