Ana Saura Kwanaki Kadan Ya Bar Mulki, Gwamna Ya Kori Kwamishina Daga Mukaminsa
- Gwamnan Edo, Godwin Obaseki, ya sallami kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Samuel Alli daga kan muƙaminsa ba tare da wani ɓata lokaci ba
- Sakataren gwamnatin jihar, Osarodin Ogie ya tabbatar da korar kwamishinan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 15 ga watan Yulin 2024
- Sanarwar ta kuma tabbatar da naɗin Dakta Roland Igbinoba a matsayin mai ba gwamna shawara na musamman kan ayyuka na musamman
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Edo - Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya kori kwamishinan lafiya, Dakta Samuel Alli.
Gwamna Obaseki ya kuma umarci Samuel Alli da ya miƙa duk wasu takardu da kayan gwamnati da ke hannunsa ga babban ma'aikacin ma'aikatar lafiya.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Osarodion Ogie, ya fitar a ranar Litinin, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Obasaki ya yi sabon naɗi a Edo
Osarodin Ogie ya kuma bayyana naɗin Dakta Roland Igbinoba a matsayin mai ba gwamna shawara na musamman kan ayyuka na musamman.
Sanarwar ta yi nuni da cewa Dakta Roland Igbinoba zai taimakawa gwamnan wajen bin diddigin ayyukan ci gaba a jihar, rahoton jaridar Independent ya tabbatar.
Gwamna Obaseki ya kori kwamishina
"Gwamnan jihar Edo, Mista Godwin Obaseki, ya amince da korar kwamishinan lafiya, Dakta Samuel Alli, nan take."
"Zai miƙa duk wasu takardu da kayan gwamnati da ke hannunsa ga babban ma’aikacin gwamnati a ma’aikatar lafiya."
"Gwamnati ta gode masa bisa ayyukan da ya yi kuma tana yi masa fatan alheri a cikin ayyukansa na gaba."
Gwamnan ya kuma amince da naɗin Dakta Roland Igbinoba a matsayin mai ba gwamna shawara na musamman kan ayyuka na musamman."
- Dakta Roland Igbinoba
An kori ƴar majalisar Edo kan shigar banza
A wani labarin kuma, kun ji cewa an kori mataimakiyar shugaban masu rinjaye ta majalisar Edo, Natasha Osawaru daga zauren majalisar saboda ta yi shigar banza.
Kakakin majalisar Edo, Blessing Agbebaku ta umarci Osawaru, mai wakiltar mazabar Egor da ta fice daga zauren majalisar bayan dan majalisa Nicholas Asonsere ya gabatar da ƙorafi.
Asali: Legit.ng