Ana Wata ga Wata: APC Ta Fadi Abin da Za Ta Yi Domin Hana Matasa Zanga Zanga
- Matasan Najeriya na cigaba da shirye shiryen fara zanga zanga domin kawo karshen tsadar rayuwa da ake fama da ita
- Jam'iyyar APC mai mulki ta yi kira na musamman ga daukacin matasan Najeriya kan dakatar da shirye-shiryen gudanar da zanga zangar
- Har ila yau, APC ta bayyana matakan da 'ya'yan jami'yyar ya kamata su dauka domin ganin ba a samu nasarar zanga zangar ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Nigeria - Yayin da shiryen-shiryen da matasa ke yi kan zanga zanga ke cigaba da kara daukan hankali, APC ta yi kira garesu.
Jami'yyar APC ta ce bai kamata a fara yin zanga zanga a wannan lokacin da Najeriya ke cikin matsalolin tsaro ba.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tsagin APC a Arewa ta tsakiyar Najeriya ce ta yi kiran ga matasan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matakin APC na hana zanga zanga
A ƙoƙarinta na ganin ba a yi zanga zanga ba, jami'yyar APC ta yi kira ga 'ya'yanta su bazama cikin al'umma domin wayar musu da kai kan illar yin zanga zangar.
APC ta kuma yi kira ga gwamnonin jihohi, masu rike da sarautu da dukkan masu fada aji a cikin al'umma su wayar da kan jama'a kan illolin zanga zangar.
Shugaban tsagin jam'iyyar APC a Arewa ta tsakiya, Alhaji Saleh Mandung Zazzaga ne ya yi kiran a yau Litinin, rahoton Daily Post.
APC ta fadi illar zanga zanga
Alhaji Saleh Mandung Zazzaga ya bayyana cewa zanga zanga yana da illoli sosai a Najeriya musamman a yankin Arewa ta tsakiya.
Shugaban ya ce yawanci zanga zanga na rikidewa zuwa rikicin addini a yankin wanda yana jawo hasara mai dimbin yawa ga al'umma.
Ya kuma bayyana cewa yankin ya dade yana fama da rikicin yan bindiga wanda kawo sabon rikici zai kai ga dagulewar lamura.
2003: Yadda malamai suka yi zanga zanga
A wani rahoton, kun ji cewa malaman addinin Musulunci a Arewacin Najeriya na cigaba da bayani kan zanga zanga da ake kokarin gudanarwa a fadin kasar.
Farfesa Salisu Shehu ya tuna baya yadda suka jagoranci zanga zanga tare da su Marigayi Sheikh Jafar Mahmud Adam a jihar Kano.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng