Kakakin Majalisa Ya Cire Tsoro Ya Fadi Abin da Ya Kawo Rashin Tsaro a Arewacin Najeriya

Kakakin Majalisa Ya Cire Tsoro Ya Fadi Abin da Ya Kawo Rashin Tsaro a Arewacin Najeriya

  • Kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya yi maganan kan matsalar rashin tsaron da ta addabi yankin Arewa maso yamma
  • Rt. Hon. Abbas Tajudeen ya ɗora alhakin matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a yankin a kan haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida
  • Ya bayyana cewa lokaci ya yi da ya kamata a ɗauki mataki kan matsalar saboda illar da take yi ga al'ummar ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya ɗora alhakin rashin tsaron da ake fama da shi a yankin Arewa maso Yamma Najeriya kan haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba.

Kakakin majalisar wakilan ya bayyana cewa kaso 80% na rashin tsaron da ake fama da shi a yankin, ya samu ne daga ayyukan haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya ji koken ƴan Najeriya, ya bada rallafin tirelolin shinkafa a jihohi 36

Abbas Tajudeen ya fadi dalilin rashin tsaro a Arewacin Najeriya
Abbas Tajudeen ya dora alhakin rashin tsaro a Arewacin Najeriya kan hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba Hoto: @Speaker_Abbas
Asali: Twitter

Menene ya haddasa rashin tsaro a Arewa?

Abbas Tajudeen ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a wajen zaman bincike kan ayyukan haƙo ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba a cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin majalisar ya koka kan yadda mutanen yankunan ba su amfana da komai face tsabagen talauci da yunwa, inda ya nuna cewa lokaci ya yi da za a ɗauki mataki.

Ya bayyana cewa haƙo ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba ya zama babban ƙaƙubale a Najeriya wanda ya jawo asarar muhalli da ƙaruwar talauci musamman a tsakanin ƙananan manoma da ba su da hanyar neman abinci da ta wuce noma.

Wasu tsiraru na sace arziƙin Najeriya

Kakakin majalisar wakilan ya bayyana cewa duk da albarkatun ƙasar da Najeriya ke da su waɗanda ya kamata su samar mata da kuɗaɗe, mafi yawan kuɗaɗen da ake samu wasu ɓata gari ne ke sace su.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya shiga taron FEC a Aso Rock, an yi shirun minti 1 saboda mutuwar Jigo

Ya bayyana cewa rahotannin da ake da su sun nuna cewa kusan kaso 80% na haƙar ma'adanai da ake yi a yankin Arewa maso Yamma ana yinsa ne ba bisa ƙa'ida ba.

A cewarsa haƙo ma'adanan a yankin shi ne maƙasudin rikice-rikicen da ake yi.

Batun kawo ƙarshen rashin tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan tsaro, Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana cewa Najeriya na daf da bankwana da rashin tsaro da ya daɗe yana ci mata tuwo a ƙwarya.

Ministan ya ce idan gwamnati ta samar da kayan aiki na zamani ga jami'an tsaro, to babu shakka an kawo ƙarshen rashin tsaro.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng