Ana Kokarin Dakatar da Tinubu Daga Bude Iyakoki, Shugaban AfDB Ya Kawo Shawara

Ana Kokarin Dakatar da Tinubu Daga Bude Iyakoki, Shugaban AfDB Ya Kawo Shawara

  • Shugaban bankin cigaban nahiyar Afirka, Akinwumi Adesina ya gargadi gwamnatin tarayya kan sababbin tsare-tsare da ta kawo
  • Akinwumi Adesina ya bayyana cewa tsare-tsaren za su jefa Najeriya cikin matsala duk da cewa gwamnatin na ganin za a samu sauki
  • Gwamnatin tarayya dai ta kawo wasu tsare-tsare ne da suka shafi harkar samar da abinci domin rage radadin rayuwa ga al'ummar kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta fara shan suka kan sabon tsarin da ta kawo na shigo da abinci daga ƙasashen ketare.

Shugaban bankin cigaban nahiyar Afirka, Akinwumi Adesina ya ce akwai kura-kurai a cikin tsarin.

Kara karanta wannan

A karshe: Tinubu ya yarda akwai yunwa a Najeriya, ya dauki sabon mataki

Akinwumi Adesina
An gargadi Bola Tinubu kan bude iyakoki. Hoto: Dr. Akinwumi Adesina.
Asali: Facebook

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Akinwumi Adesina ya fadi haka ne a wani coci a birnin tarayya Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane tsari shugaba Bola Tinubu ya kawo?

Gwamnatin Tinubu dai ta kawo tsari ne na shigo da kayan abinci da ake amfani da su yau da kullum a Najeriya.

Ministan noma ne ya bayyana tsarin a ranar 10 ga watan Yuli inda ya ce za a cire haraji na kayan abincin na tsawon kwanaki 150.

Martanin Akinwumi Adesina ga Tinubu

Shugaban ADB, Akinwumi Adesina ya ce wannan matakin da gwamnatin ta dauka na bude iyakoki domin shigo da abinci abin takaici ne matuka.

Akinwumi Adesina ya ce wannan matakin zai mayar da dukkan kokarin da aka yi na ciyar da Najeriya gaba a harkar noma baya.

Adesina: 'Najeriya ta tsaya da kafafunta'

Kara karanta wannan

An jefi Ali Ndume da rashin ladabi ga Tinubu saboda ya yi magana kan yunwa

Akinwumi Adesina ya ce bai kamata a mayar da Najeriya kasar da take dogaro da abinci daga ketare ba, rahoton Channels Television.

Ya ce shigo da abinci ba zai magance matsalolin tashin farashi ba saboda haka ya kamata Najeriya ta ciyar da kanta.

An samu saukin abinci a jihohi

A wani rahoton, kun ji cewa yayin da ake fama da tsadar kayayyaki musamman bangaren abinci, an fara samun sauki a wasu jihohin Arewacin Najeriya

Rahotanni sun nuna cewa jihohin da aka samu saukin idan aka kwatanta da kwanakin baya sun hada da Gombe da Jigawa da kuma jihar Bauchi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng