Jira Ya Kare: Tinubu Ya Sanya Lokacin Kaddamar da Shirin Ba Dalibai Rance
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai ƙaddamar da shirin ba da rance ga ɗalibai a ranar Laraba, 17 ga watan Yulin 2024
- Shugaban ƙasan zai ƙaddamar da shirin ne wanda aka daɗe ana jiran fara aikinsa a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja
- A kwanakin baya ne Shugaba Tinubu ya amince da fitar da Naira biliyan 35 domin ƙaddamar da tallafi ga ɗalibai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai ƙaddamar da shirin ba da rance ga ɗalibai.
Shugaban ƙasan zai ƙaddamar da shirin ne a ranar Laraba, 17 ga watan Yulin 2024 wanda zai sanya a fara aiwatar da shirin.
Ɗalibai za su samu rance daga gwamnati
Jaridar Leadership ta rahoto cewa za a ƙaddamar da shirin ba da rancen ne ga ɗalibai a fadar shugaban ƙasa da ke Aso Rock Villa, a birnin tarayya Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwanan nan Shugaba Tinubu ya amince da Naira biliyan 35 domin ƙaddamar da shirin, wanda ɗalibai 70,000 za su amfana da shi a karo na farko.
Asusun NELFUND mai kula da ba da rancen ga daliɓai, ƙarƙashin jagorancin Jim Ovia, ta amince da bayar da lamunin ga waɗanda suka yi nasara a taron farko da ta yi a Abuja a watan jiya, rahoton jaridar The Sun ya tabbatar.
Shugaba Tinubu zai tallafawa ɗalibai
Shirin bayar da lamuni ga ɗalibai, wani tsari ne na gwamnatin Tinubu, wanda yake da nufin bayar da tallafin kuɗi ga ɗaliban da suka cancanta a duk fadin ƙasar nan ta fannin kuɗaɗen makaranta da alawus.
Sama da dalibai miliyan 1.2 ake sa ran za su amfana daga kashi na farko na shirin.
An caccaki Sanata kan sukar Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gamayyar ƙungiyar dattawan Arewa maso Gabas (CNEF) ta yi zargin cewa shekara 20 da Sanata Ali Ndume ya yi a majalisar tarayya bai amfani jihar Borno ba.
Ƙungiyar dattawan ta buƙace shi da ya daina sukar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ko ta sanya ya rasa kujerarsa a zaɓen 2027.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng