Gwamna Ya Duba Halin da Mutane Ke Ciki, Ya Karya Farashin Kayan Noma ga Talakawa

Gwamna Ya Duba Halin da Mutane Ke Ciki, Ya Karya Farashin Kayan Noma ga Talakawa

  • Yayin da damina ta kankama Gwamna Bala Mohammed ya kaddamar da sabon shirin tallafawa manoma a jihar Bauchi
  • Gwamnan ya bayyana cewa shirin zai sayar da takin zamani a kan N20,000 kuma zai samar da sauran kayayyakin noma a farashi mai sauƙi
  • Haka nan kuma gwamnatin Bauchi ta ce za ta kafa cibiyoyin kiwon dabbobi domin kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya kaddamar da shirin noma na 2024 domin taimakawa manoma da takin zamani a farashi mai rahusa.

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta sayarwa manoman Bauchi takin zamani na NPK kan kowane buhu a kan N20,000 kuma za a rage tsadar kayan noma.

Kara karanta wannan

Shehin malami ya musanta karbar N16m daga Tinubu, ya fadi dalilin ziyartar shugaban kasa

Gwamna Bala Mohammed.
Gwamnatin Bauchi ta bullo da tallafin noma domin rage farashin kayayyaki ga manoma Hoto: Senator Bala Mohammed
Asali: Facebook

Gwamna ya sanar da karya takin noma

A wurin kaddamar da shirin a garin Dass, Bala Mohammed ya ce gwamnatin Bauchi ta ware N300m domin inganta harkokin noma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da gwamnan ya wallafa a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter.

Gwamna Mohammed ya ce sabon shirin zai maida hankali wajen bullo da hanyoyin bunƙasa noma kuma zai samar da sinadarai da kayan noma na N50m.

Ya kuma yabawa ACRESAL, shirin noman da ya fi shahara a Bauchi, inda ya jaddada kudirinsa na aiwatar da ingantaccen tsarin noman zamani a faɗin jihar.

Bauchi ta karɓo bashi daga bankin duniya

Gwamnan ya bayyana cewa jihar Bauchi ta zama jiha ta farko a kasar nan da ta samu rance daga bankin duniya.

"Za a yi amfani da bashin wajen kafa cibiyoyin kiwon dabbobi a Bauchi, muna sa ran wannan matakin zai kawo sauyi a harkar kiwo a da kuma inganta ayyukan manoma."

Kara karanta wannan

"Gwamnatin Tinubu ta zuba ido ana kashemu," Dattawan Katsina sun dauki zafi

- Gwamna Bala Mohammed

Bala Mohammed ya ƙara da cewa gwamnatin jihar za ta kafa cibiyoyin sarrafa kayan noma domin rage asarar da ake samu bayan girbi da kuma inganta darajar amfanin gona.

A cewarsa hakan zai kara yawan kuɗin shiga ga manoma da kuma rage asarar kayan abinci.

BUA zai gina katafaren asibiti a Bauchi

A wani rahoton kuma Mai kamfanin BUA, Abdulsamad Rabi'u ya dauki kudurin samar da katafaren asibitin zamani ga jami'an kwastam a Bauchi.

A jiya Litinin ne aka daura tubalin ginin asibitin inda ya samu halartar manyan jami'an gwamnati da al'ummar yankin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262