'Yan Majalisa Sun Jikawa Gwamna Aiki Bayan Hana Shi Kashe Kudi, Sun Kafa Sharadi
- Majalisar dokokin jihar Rivers ta ɗauki mataki bayan wa'adin kwana bakwai da ta ba Gwamna Siminalayi Fubara ya cika kan sake gabatar da kasafin kuɗin 2024
- Ƴan majalisar masu biyayya ga Nyesom Wike ƙarƙashin jagorancin Martins Amaewhule sun haramtawa gwamnan kashe kuɗaɗen jihar
- Sun kuma rufe asusun tattara kuɗaɗen shiga na jihar har sai zuwa lokacin da Gwamna Fubara ya sake gabatar musu da kasafin kuɗin a gaban majalisar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Rivers - Majalisar dokokin jihar Rivers ƙarƙashin jagorancin Martin Amaewhule ta dakatar Gwamna Siminalayi Fubara daga kashe kuɗaɗen jihar.
Majalisar ta dakatar da gwamnan ne daga kashe kuɗaɗen har sai ya sake gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2024 a gabanta.
Ƴan majalisa sun hana gwamna kashe kuɗi
Jaridar The Nation ta kawo rahoto cewa ƴan majalisar sun cimma wannan matsayar ne a yayin zamansu na ranar Litinin, 15 ga watan Yulin 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannnan umarnin dai na zuwa ne bayan wa'adin da ƴan majalisar masu biyayya ga ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, suka ba gwamnan na kwana bakwai ya cika kan sake gabatar da kasafin kuɗin.
Tashar Channels tv ta ce shugaban masu rinjaye na majalisar, Major Jack, shi ne ya gabatar da ƙudirin domin sanar da majalisar cewa wa’adin kwanaki bakwai domin sake gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2024 ga majalisar ya cika.
Bayan nazari, majalisar ta yanke shawarar rufe asusun tattara kuɗaɗen shiga na jihar Rivers, tare da haramtawa gwamnatin Gwamna Fubara kashe kuɗaɗen jihar.
Tun da farko dai Gwamna Fubara ya yi watsi da wa'adin da ƴan majalisar suka ba shi, inda ya bayyana su a matsayin waɗanda ba halastattun ƴan majalisa ba.
APC ta shawarci Gwamna Fubara
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar adawa ta APC a jihar Rivers, ta yi kira ga Gwamna Siminalayi Fubara da ya mutunta hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke kan ƴancin cin gashin kan ƙananan hukumomi.
Ta buƙace shi da ya rushe shugabannin riƙo da ya naɗa a ƙananan hukumomin saboda hakan ya saɓa doka biyo bayan hukuncin kotun.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng