Sojoji Sun Yi Luguden Wuta Kan Ƴan Ta’adda a Arewa, Sun Faɗi Nasarar da Aka Samu

Sojoji Sun Yi Luguden Wuta Kan Ƴan Ta’adda a Arewa, Sun Faɗi Nasarar da Aka Samu

  • Rundunar sojin saman Najeriya ta bayyana yadda tayi wa 'yan ta'adda luguden wuta ta jiragen yakinta na sama a jihar Kaduna
  • Rundunar ta ce an samu gagagrumar nasara yayin da aka halaka 'yan ta'adda a kananan hukumomin Giwa da Igabi na jihar
  • Bidiyon bayan luguden ya nuna konanun bukkokin 'yan ta'addan, gawarwaki da kuma yadda luguden ya kone rufin jinkarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Rundunar sojin saman Najeriya ta ce an halaka 'yan ta'adda masu yawa a ruwan wutan da aka yi musu ta sama a kananan hukumomin Giwa da Igabi na jihar Kaduna.

A wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi, Edward Gabkwet, mai magana da yawun rundunar NAF, ya ce an kai samamen ta sama a cikin atisayen Whirl Punch.

Kara karanta wannan

Ranar Ashura: An tsananta tsaro a Kaduna, ƴan sanda sun haramta taron ƴan Shi'a

Rundunar sojin saman Najeriya ta yi magana kan yaki da 'yan ta'adda a Kaduna
Sojin sama sun yi lugude kan 'yan bindiga a Kaduna, sun samu nasara. Hoto: @NigAirForce
Asali: Twitter

Edward Gabkwet ya ce an halaka 'yan ta'adda masu yawa yayin da rufin jinkar bukkokinsu suka sha ruwan wuta a karamar hukumar Giwa a ranar 12 ga Yuli, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"An babbake bukkokin 'yan ta'adda" - Gabkwet

"A daya daga cikin luguden da aka yi ranar 12 ga Yulin 2024 a maboyar 'dan ta'adda Alhaji Layi da ke kauyen Kufan Shantu a karamar hukumar Giwa, an halaka 'yan ta'adda masu yawa.
"An lura cewa rufin jinkar dake saman bukkokinsu duk sun kone kurmus. Hakazalika, an lalata dukkanin kayan aikinsu da suka boye a kasan bishiyoyi."

- A cewar sanarwar.

Dajin Malum ya sha ruwan wuta

Jaridar The Cable ta sanar da cewa, yayin luguden wutan da aka yi a Dajin Malum da ke karamar hukumar Igabi a ranar 13 ga Yuli, an kashe 'yan ta'addan da ke sha'aninsu a dajin.

Kara karanta wannan

Fashin magarkama: 'Yan Boko Haram sama da 100 sun tsere daga gidan yarin Nijar

Edward Gabkwet ya kara da cewa:

"A yayin da ake duba bidiyon harin da za a kai, an ga 'yan ta'addan suna kai wa da kawowa a wani gida mai ginin kwano."
"Daga nan ne aka ba da izinin kai harin, wanda ya kakkabe da yawan 'yan ta'addan kamar yadda bidiyon luguden wutar ya nuna."

Kakakin rundunar sojin saman ya tabbatar da cewa rundunar za ta yi aiki da rundunar kasa domin tabbatar da sun kakkabe 'yan ta'adda a yunkurin samar da tsaro da zaman lafiya.

'Yan ta'adda sun tsere daga gidan yari

A wani labari na daban, mun ruwaito cewa wani abu kamar fashin magarkama ya faru a gidan Koutoukale da ke Arewacin kasar Nijar inda ya jawo tserewar 'yan ta'adda sama da 100.

An ce lamarin mai cike da sarkakiya ya faru ne a daren jiya Ahamis, 11 ga watan Yulin 2024 wanda ya jefa fargaba a zukatan jama'ar da ke a yammacin kasar.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda a jihohi, sun kwato makamai da dama

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.