'Yan Bindiga Na Kokarin Hana Noma, Sun Kakaba Harajin N200m Kan Wasu Kauyuka a Arewa

'Yan Bindiga Na Kokarin Hana Noma, Sun Kakaba Harajin N200m Kan Wasu Kauyuka a Arewa

  • Ƴan bindiga sun taso mutanen wasu ƙauyukan ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara a gaba bayan sun ƙaƙaba musu haraji
  • Ƴan bindigan sun sanya harajin N200m kan ƙauyuka 10 na ƙaramar idan suna son su tsira da rayukansu
  • Mazauna yankin sun bayyana cewa tuni wasu ƙauyukan suka fara biyan kuɗaɗen yayin da sauran ke ta fafutuka wajen ganin sun biya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Ƴan bindiga sun saka harajin kusan N200m kan wasu ƙauyuka a ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.

Galibin ƙauyukan da abin ya shafa su na kusa da garin Kaura Namoda-Moriki a ƙaramar hukumar Zurmi.

'Yan bindiga sun sanya haraji a Zamfara
'Yan bindiga sun sanya haraji kan wasu kauyuka a Zamfara Hoto: @Mfareees
Asali: Twitter

Ƴan bindiga sun sanya haraji a Zamfara

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bi dare sun hallaka mutum 1 da sace wasu mutum 4 a wani hari

Jaridar Daily Trust ta ce ƙauyukan da abin ya shafa da harajin da za su bayar sun haɗa da Yan Dolen Kaura (N15m), Gidan Zagi (N15m), Kanwa (N20m), Kaiwa Lamba (N26m).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sun haɗa da Gidan Dan Zara (N22m), Jinkirawa (N16m), Dumfawa (N16m), Ruguje (N7m), Babani (N3m) da Gidan Duwa (N4m).

Mazauna ƙauyukan sun ce suna fuskantar matsin lamba kan su tara waɗannan kuɗaɗen cikin wani kayyadadden lokaci.

An fara biyan harajin 'yan bindiga

An tattaro cewa tuni wasu ƙauyukan suka biya kuɗaɗen harajin nasu, yayin da wasu kuma ke ta fafutuka domin tattara kuɗaɗen da ake buƙata.

Wani mazaunin garin Zurmi mai suna Malam Yunusa Musa ya shaidawa jaridar cewa harajin zai fara aiki daga wannan makon.

"Abin takaicin shi ne mazauna garin Turawa sun biya N15m amma ƴan bindigan ba su sako mutanensu ba. Kauyuka da dama waɗanda harajin su yake tsakanin N26m zuwa N3m tuni sun biya kuɗin."

Kara karanta wannan

Daga karshe Gwamna Zulum ya fadi dalilin kai harin kunar bakin wake a Borno

- Malam Yunusa Musa

Wani mazaunin garin Malam Haruna Ilu ya ce mazauna wasu ƙauyukan da lamarin ya shafa sun fara tururuwa zuwa garuruwa da birane domin neman abin yi saboda su tara kuɗaɗen.

Karanta wasu labaran kan ƴan bindiga

Ƴan bindiga sun kai hari a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun kai hari tare da yin garkuwa da mutane 47 daga kauyen Danbaza a karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.

Wani mazaunin ƙauyen, Abdul Danbaza, ya bayyana cewa ƴan bindigan sun mamaye garin da misalin ƙarfe 2:30 na daren ranar Laraba, 26 ga watan Yunin 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng