'Yan Bindiga Sun Bi Dare Sun Hallaka Mutum 1 da Sace Wasu Mutum 4 a Wani Hari
- Ƴan bindiga sun kai hare-hare a jihar Anambra a cikin daren ranar Asabar, 13 ga watan Yuli inda suka tafka ɓarna
- Miyagun ƴan bindigan sun hallaka mutum ɗaya tare da sace wasu mutum huɗu yayin hare-haren da suka kai
- Rundunar ƴan sandan jihar Anambra ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta bayyana cewa ana ƙoƙarin ceto mutanen
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Anambra - Ƴan bindiga sun yi garkuwa da aƙalla mutum huɗu a yayin wani hari a jihar Anambra.
Ƴan bindigan sun kuma hallaka wani mutum ɗaya a hare-haren da suka kai a daren ranar Asabar, 13 ga watan Yulin 2024.
Yadda ƴan bindigan suka kai hare-haren
Jaridar The Nation ta rahoto cewa lamarin ya auku ne a wurare daban-daban na jihar da ke yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tattaro cewa a Ifite Awka, kusa da ƙofar jami'ar Nnamdi Azikiwe (UNIZIK), an sace mutum biyu bayan ƴan bindiga sun buɗe wuta.
Ƴan bindigan sun kuma yi garkuwa da wani mutum da yamma a kan titin Agulu-Oraukwu na Peter Obi.
An tattaro cewa lamarin ya fi tayar da hankali ne da daddare a kasuwar Oye, Nimo, cikin ƙaramar hukumar Njikoka, inda ƴan bindigan suka yi garkuwa da wani mutum guda, cewar rahoton jaridar The Punch.
A ƙauyen Enuavomimi, Enugwu-Ukwu, da ke Njikoka, maharan sun kashe wani mutum mai suna Clement Eduzor.
Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, Ikenga Tochukwu, ya tabbatar da aukuwar ɗaya daga cikin hare-haren amma bai ce komai ba kan sauran.
"Kwamishinan ƴan sandan jihar Anambra, Nnaghe Obono Itam ya bayyana cewa ana ci gaba da ƙoƙarin kamo maharan tare da kubutar da wadanda lamarin ya shafa a ranar 13/7/2024 da aka sace a kan titin Ifite-Amansea, Awka."
- Ikenga Tochukwu
Ƴan bindiga sun sace shugaban kwaleji
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da ma’aikata uku da suka haɗa da mukaddashin shugaban kwalejin fasaha ta jihar Benue, da ke Ugbokolo, Dakta Emmanuel Barki.
Emmanuel Barki da sauran ma'aikata biyu na kwalejin da direbansu, an sace su ne a kan hanyar su ta dawowa zuwa Ugbokolo bayan sun je wani aiki a Makurdi.
Asali: Legit.ng