Tsadar Rayuwa: Sheikh Gumi Ya Lissafa Ka’idoji 6 Na Gudanar da Zanga Zangar Lumana
Jihar Kaduna - A yayin da shirin matasan Najeriya da ma dattawa na gudanar da zanga-zanga a fadin kasar nan ya ke ci gaba da karade duniyar intanet, Sheikh Ahmad gumi ya yi martani.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Fitaccen malamin addinin Musuluncin ya ce lallai akwai bukatar al'ummar Najeriya su yi taka tsan-tsan yayin da suka shirya gudanar da zanga-zangar.
Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar daren ranar Asabar, Sheikh Gumi ya ce matasa su gudanar da zanga-zanga kawai idan sun cika sharudda shida.
Malamin addinin ya jaddada cewa yin zanga-zangar lumana bai sabawa doka ba ma damar aka yi ta bisa doton dokar, inda ya nemi matasa da su kai zuciya nesa tare da gujewa karya doka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ga jerin ka'idoji shida na yin zanga-zangar lumana:
1. Amfani da shugabanni masu mutunci
Sheikh Gumi ya ce idan ana son zanga-zangar ta yi nasara, dole ne masu zanga-zangar su samu shuwagabanni masu mutunci da za su jagorantar zanga-zangar.
Ya ce a jinkirta zanga-zangar ma damar babu jagororin kwarai a ciki saboda akwai yuwuwar bata gari su yi amfani da damar wajen tayar da zaune tsaye, kuntata jama'a ko mayar da abun siyasa.
2. A gabatar da bukatu a rubuce
Abu na biyu shi ne bayyana buƙatun zanga-zangar a rubuce waɗanda yakamata su kasance masu sauƙin fahimta kuma a kan tsarin hakkin kowanne dan kasa kamar yadda yake a doka.
"Kar a nemi murabus din shugabannin da tsarin mulki ya yarda da su, yin hakan zai iya haifar da rashin zaman lafiya wanda da zama mafi muni fiye da matsalolin tattalin arziki."
- Inji malamin addinin.
3. Rufe tituna yayin zanga-zanga
Kada masu zanga-zanga su toshe hanyoyi tare da hana masu ababen hawa wucewa saboda hakan zai cutar da mutanen da ake ƙoƙarin nemarwa 'yancin su.
4. Ayi abin da ya dace a watse
Malamin addinin Musuluncin ya nemi masu zanga-zangar da su gabatar da bukatunsu ga hukumomin da abin ya shafa kuma ku watse cikin mutunci bayan hakan.
5. Ka da a yarda da bara gurbi
Sheikh Ahmad gumi ya kuma ce masu zanga-zangar su yi adawa da duk wani mai zanga-zangar da ke son haifar da hargitsi ko yake kokarin tunzura jama'a.
6. Idan akwai matsala, a hakura
Ka'ida ta karshe a cewar fitaccen malamin addinin ita ce idan har wadannan ka'idoji na 1 zuwa na 5 basu samu ba, ko ba za a iya cimma su ba, to a hakura da zanga-zangar zai fi alkairi.
A yayin da yake addu'ar Allah ya gyara tattalin arzikin kasar, Sheikh Gumi ya yi kira ga gwamnati da ta gaggauta duba bukatun matasan tare da yin mai yiwuwa domin hana yin zanga-zangar.
Duba bayanin malamin a kasa:
Malamai sun rarrabu kan halaccin zanga-zanga
A wani labarin, mun ruwaito cewa malamai a Najeriya na cigaba da bayyana ra'ayoyi mabanbanta kan shirin fita zanga-zanga da matasa ke yi.
An samu rarrabuwar kai tsakanin malamai kasancewar wasu sun goyi bayan lamarin wasu kuma sun nuna bai dace ba. Legit Hausa ta kawo jerin matsayar malaman.
Asali: Legit.ng