Tsadar Abinci: Fitaccen Basarake Ya Yi Maganin Abin, Ya Dauki Mataki Kan ’Yan Kasuwa

Tsadar Abinci: Fitaccen Basarake Ya Yi Maganin Abin, Ya Dauki Mataki Kan ’Yan Kasuwa

  • A kokarin kawo karshen tsadar kayan abinci, Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi ya dauki mataki kan 'yan kasuwa a Osun
  • Basaraken ya haramta duk wasu kungiyoyin 'yan kasuwa a Ile-Ife inda ya ke zarginsu da saka farashin kayan abinci
  • Wannan na zuwa ne yayin aka yi bincike tare da gano 'yan kasuwar na zama a ofisoshi domin saka farashi yadda suke so

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Osun - Sarkin Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi ya haramta kungiyoyi da ke cikin kasuwannin garin gaba daya.

Basaraken ya dauki matakin ne domin dakile yawan tashin farashin kaya da ya ke zargin kungiyoyin.

Basarake ya dauko hanyar dakile tsadar abinci a kasuwanni
Sarkin Ile-Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi ya haramta kungiyoyin 'yan kasuwa kan zargin kara farashi. Hoto: Ooni Adimula of Ife.
Asali: Twitter

Basarake ya haramta kungiyoyin 'yan kasuwa

Kara karanta wannan

Kamar al'amara: Yadda barawo ya yaudari direban kabu-kabu da farfesa, ya sace motarsa

Shugaban wata kasuwa a Ile-Ife da ke jihar Osun, Akinwande Olajire shi ya tabbatar da haka, kamar yadda Punch ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Olajire ya ce basaraken yana zargin kasancewar kungiyoyin yana da matukar tasiri wurin kara farashin kaya musamman na abinci.

Ya ce akwai wasu 'yan kasuwa da suke siyar da kayan abinci da ake zargin suna saka farashin kaya yadda suke so, cewar The Guardian.

Basaraken na zargin 'yan kasuwa da kara farashi

Har ila yau, ya ce ana zarginsu da siyan kayan musamman na abinci cikin farashi mai sauki amma suna siyarwa da tsada.

"Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi ya tura ni zuwa kasuwanni da ke cikin garin Ife baki daya."
"Basaraken da sauran 'yan Majalisarsa sun fahimci ana kara kudin kaya, daga cikin matakin farko na dakile hakan shi ne haramta kungiyoyi."

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi sabon albashin da zai iya biyan ma'aikata, NLC ta dage kan N250,000

- Akinwande Olajire

Akinwande ya ce sun dauki matakin rurrufe wasu wuraren da ake gudanar da ganawa domin saka farashin kaya inda ya ce idan aka kama wani dan kasuwa da laifin zai fuskanci fushin hukuma.

Gwamna Makinde ya bukaci kawo karshen yunwa

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Seyi Makinde ya koka kan yadda yunwa da wahalar rayuwa suka yi yawa a Najeriya.

Gwamnan jihar Oyo ya bayyana hakan ne yayin martani kan hukuncin kotu game da 'yancin kananan hukumomi a kasar.

Ya ce an kawo maganar kananan hukumomin ne domin kawar da hankulan jama'a kan abubuwan da suke faruwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.