A Karo na 2, Gwamnatin Abba Gida Gida ta Fara Rabon Tallafin Kudi ga Mata 5,200

A Karo na 2, Gwamnatin Abba Gida Gida ta Fara Rabon Tallafin Kudi ga Mata 5,200

  • Gwamnatin Kano ta fara rabon kudi ga mata 5,200 daga kananan hukumomi 44 a jihar da zummar rage talauci tsakaninsu
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya raba tallafin N50, 000 ga matan domin habaka jarinsu wanda ake sa ran zai bunkasa kasuwancin da su ke yi
  • Mata 100 aka zabo daga kananan hukumomi 36 da ke wajen jihar, yayin da aka bawa mata 200 a kowacce karamar hukumar cikin birni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Kano - Gwamnatin Kano ta kaddamar da rabon tallafin N50,000 ga mata da su ka fito daga kananan hukumomi 44 na jihar. Wannan shi ne karo na biyu da gwamnan ke raba tallafin, inda a wannan lokacin aka raba N260m a ci gaba da kokarin rage talauci tsakanin mata.

Kara karanta wannan

"Hana makiyaya kiwo a sake zai jawo manyan matsaloli 3 a ƙasa," KACRAN

Abba Kabir Yusuf
Gwamnatin Kano ta raba wa mata 5,200 tallafin N260m Hoto: Sunusi Bature Dawakin Tofa
Asali: UGC

Wannan na kunshe cikin sanarwar da darakta janar kan yada labaran gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dalilin raba tallafi ga mata

Gwamnatin Kano ta ce tana raba tallafi N50,000 ga mata a kananan hukumomin jihar domin habaka kasuwancinsu. Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa a wannan karon, mata 100 daga kananan hukumomi 36 na jihar na daga cikin wadanda su ka samu tallafin. Yayin da mata 200 daga cikin kowacce karamar hukumar da ke cikin birni guda takwas aka bawa tallafin na wannan lokaci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Tallafin zai rage talauci," Abba gida-gida

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa tallafin N50,000 ga watan jihar da gwamnatinsa za ta rika bayarwa duk wata zai taimaka wajen rage talauci.

Gwamna Abba gida-gida ya hori matan da su yi amfani da kudin wajen kara jari domin habaka tattalin arzikinsu sannu a hankali.

Kara karanta wannan

Ana dab da zabe: An harbi tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump a wani taro a Pennsylvania

Gwamna ya raba tallafin abinci

A baya mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Kaduna ta raba tallafin kayan abinci ciki har da masara da shinkafa tirela 128.

Gwamnan jihar Uba Sani ya bayyana cewa haka kuma za a raba tallafin kudi N11.4bn ga masu kanana da matsakaitan sana'o'i.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.