Zaune Bata Kare Ba: Har Yanzu da Sauran Mutane a Kasa Duk da Ceto Mutum 4 da Gini Ya Danne a Abuja

Zaune Bata Kare Ba: Har Yanzu da Sauran Mutane a Kasa Duk da Ceto Mutum 4 da Gini Ya Danne a Abuja

  • Rahoton da muke samu daga Abuja ya bayyana cewa, a halin yanzu an ceto mutum hudu daga cikin ginin da ya rushe kan jama’a a birnin
  • An ruwaito a baya cewa, wani bene ya fadi a Abuja, ya danne mutane da dama da har yanzu ake kokarin ceto su
  • Wannan ne karo na biyu da ake samun rugujewar gini a Najeriya a cikin kasa da mako guda a wannan watan na Yuli

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

FCT, Abuja - An ceto mutane hudu da ransu daga baraguzan ginin bene mai hawa biyu da ya ruguje a kusa da otal din Cupid, a titin Sultan Dansuki da ke Kubwa a karamar hukumar Bwari.

Kara karanta wannan

Kawo karshen tsadar mai: Dillalan man fetur sun ba da shawarar yadda man fetur zai koma N620

Hukumar bayar da agajin gaggawa na FCT (FEMD) ta tabbatar da faduwar ginin da misalin karfe 6:45 na safe, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

An ceto wadanda gini ya rushe da su a Abuja
An ceto mutum da gini ya danne a Abuja | Hoto: @eonsintelligenc
Asali: Twitter

Biyu daga cikin wadanda aka ceto, FEMD ta ce an kai su babban asibitin Kubwa don gaggauta duba halin da suke ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har yanzu akwai sauran mutane a kasan gini

Ana ci gaba da kokarin neman sauran mutanen da suka makale a karkashin tare da ceto daga kasan baraguzan ginin.

A halin da ake ciki, kusan dukkan hukumomin ba da agaji da na kashe gobara sun hallara a wurin, inda suke kokarin aikin ceto.

Mutane nawa ne a cikin ginin da ya ruguje?

A cewar FEMD a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ta Nkechi Isa ya fitar, ta ce akalla akwai dakuna 45 masu cin gashin kansu a ginin, rahoton Channels Tv.

Kara karanta wannan

Mutane da dama sun makale yayin da gini ya rufto musu a Abuja, an samu bayanai

A baya an yi amfani da dakunan a matsayin otal kafin daga bisani a maida shi gidajen zaman al’umma.

Darakta Janar na FEMD, Misis Florence Dawon Wenegieme da ke wurin da lamarin ya faru ta ce za a ci gaba da aikin ceto har sai an zo karshen kasan ginin don tabbatar da ba a bar mutane a kasanshi ba.

Wenegieme ta yi kira ga masu gine-gine da su bi ka’idojin inganta gini da hukumomi ke bayarwa a duk sadda suke aikin gine-ginensu.

An rufe makaranta a Jos bayan gini ya danne dalibai

A wani labarin, gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato ya sanar da rufe makarantar sakandire ta Saint Academy nan take bayan ruftawar gini ranar Jumu'a.

Gwamnan ya kuma bayar da umarnin a gudanar da bincike mai zurfi kan ibtila'in rugujewar ginin makarantar wanda ya yi sanadin mutuwar ɗalibai 22 da raunata wasu 132.

Gwamnan ya bada umarnin rufe makarantar ne a lokacin da ya ziyarci harabar ginin da ya ruguje domin tantance halin da ake ciki, kamar yadda Channels tv ta kawo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.