Kawo Karshen Tsadar Mai: Dillalan Man Fetur Sun Ba da Shawarar Yadda Man Fetur Zai Koma N620
- Dillalan man fetur a Najeriya neman kamfanin gwamnati na man fetur, NNPC ya ware masu 50% na man fetur da ake samu don amfanin kasar
- Wannan na zuwa ne daidai lokacin da ake fuskantar karancin mai a kasar, wanda ya haifar da tashin farashinsa a gidajen mai
- Ya bayyana cewa mambobin IPMAN suna siyan man fetur daga hannun wasu masu siyar da mai farashin mai tsanani wanda ke tada farashin mai a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
FCT, Abuja - Domin rage tsadar man fetur da kuma layuka a gidajen mai, kungiyar dillalan man fetur ta IPMAN ta roki NNPC da ta ke ware masu kaso 50% na man kasar.
Wannan na zuwa ne a cikin wata hira da mataimakin shugaban kungiyar, Hameed Fasola a ranar Juma’a, inda ya bayyana kadan daga abubuwan ke jawo layuka da tsadar mai a kasar.
A cewarsa, mambobin IPMAN na siyan man fetur da tsada daga hannun masu shigo da mai, wanda ya sa su ma suke siyar da man a tsattsauran farashi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mataimakin shugaban ya ce kungiyar ta roki NNPC da ta kara kason da take warewa ‘ya’yanta don samar da wadataccen man fetur mai rahusa da kuma rage layuka a gidajen mai, rahoton TheCable.
Za a iya siyar da man fetur N620, inji IPMAN
Da yake bayyana yadda ake samar da mai a kasar da kuma yadda yake shafar farashin man fetur a gidajen man kasar nan.
Ya bayyana cewa, IPMAN za ta iya siyar da man fetur daga N720 zuwa N620 idan za a samu wadatar man daga kamfanin na NNPC.
Hakazalika, ya ce rashin wadatuwar man fetur din ya sa wasu gidajen mai sun rufe kasuwancinsu, wanda hakan ke kara jefa ‘yan kasa a tsananin rashin mai.
An kama jaragun man fetur za a fitar dasu Kamaru
A bangare guda, a lokacin da 'yan Najeriya ke fama da dawowar layukan mai, hukumar kwastam ta cafke wasu dauke da fetur da za a yi safararsa zuwa kasar waje.
Jami'an hukumar kwastam da ke kula da shiyyar Adamawa/Taraba ne su ka cafke wadanda ake zargi da safarar fetur din.
Jaridar The Nation ta wallafa cewa an kama mota da ganguna 85 dauke da lita 200 kowanne na fetur.
Asali: Legit.ng