Sabuwar Tafiya: Hotunan Yadda Kwankwaso Ya Kaddamar da Sabon Tambarin NNPP a Abuja

Sabuwar Tafiya: Hotunan Yadda Kwankwaso Ya Kaddamar da Sabon Tambarin NNPP a Abuja

  • Jam'iyyar NNPP ta yi sabon tambari bayan rasa nasara a zaben 2023 da ya gabata, an kaddamar a Abuja
  • Kwankwaso ya bayyana manufar sauya tambarin daga mai alamar kayan marmari zuwa wani nau'in daban
  • Ya kuma mika muhimmin sako ga 'yan Najeriya kan manufofin ci gaba da jam'iyyar ke da shi ga kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP a zaben 2023, Rabiu Musa Kwankwaso ya halarci taron kaddamar da sabon tambarin jam'iyyar ta NNPP.

Kwankwaso ya yada hotunan yadda aka gudanar da bikin kaddamar da sabon tambarin ne a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya faɗi jihar da za ta fara amfani da sabon tambarin NNPP a Najeriya

Kwankwaso yadda aka sauya tambarin NNPP
Yadda aka sauya tambarin NNPP zuwa jan launi | Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

A kalamansa, cewa ya yi:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Na samu karramawar kaddamar da sabon tambarin jam’iyyar NNPP, da aka aminta da ita, yau a Abuja."

Dalilin da ya sa aka sauya tambarin NNPP

Da yake bayyana dalilin sauya tambarin jam'iyyar, Kwankwaso ya ce gudanar NNPP ce ta yanke shawarin sauya tambarin tare da sake saita manufofin jam'iyyar.

Ya kuma ce, an yanke wannan shawarin ne bayan kammala fafatawa da jam'iyyar ta yi a zaben 2023 da ya wakana bara.

Idan baku manta ba, jam'iyyar NNPP ce ta zo na hudu a zaben shugaban kasa da aka gudanar a bara biyo bayan jam'iyyun APC, PDP da Labour.

Sakon da sabon tambarin NNPP ke isarwa

Sabon tambarin jam'iyyar na nuni da wanzuwar ilimi a Najeriya da kuma tsayuwar jam'iyyar kekam kan yada zaman lafiya da ci gaban kasa.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi martani kan korarsa a NNPP, ya fadi matsalar da suka fuskanta a zabe

Daga karshe, Kwankwaso ya mika sakon godiya ga hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) kan amincewa cikin gaggawa da tambarin.

Hakazalika, ya bukaci 'yan Najeriya da su ci gaba da nuna goyon baya da kuma kwarin gwiwarsa kan jam'iyyar NNPP.

Jihar da za ta fara amfani da sabon tambarin NNPP

Kun ji cewa, Kwankwaso ya bayyana jihar Ondo a matsayin jihar da za ta fara amfani da sabon tambarin jam'iyyar NNPP.

Ya bayyana hakan ne a bikin kaddamar da sabon tambarin a babban birnin tarayya Abuja a ranar Juma'a.

Kwankwaso ne daya daga jiga-jigan NNPP da ke ci gaba da tallata jam'iyyar a fadin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.