NLC: Rigima Ta Ɓarke Tsakanin Ƴan Kwadago Yayin da Ake Tsaka da Batun Ƙarin Albashi

NLC: Rigima Ta Ɓarke Tsakanin Ƴan Kwadago Yayin da Ake Tsaka da Batun Ƙarin Albashi

  • Rigama ta ɓalle a tsakanin ƴan kwadago yayin da mutum biyu suka fara ikirarin shugabancin ƙungiyar NLC reshen jihar Ondo
  • Wasu ƙungiyoyin ma'aikata 22 sun zaɓi Kwamared Olapade Ademola a matsayin sabon shugaban NLC ta jihar bisa hujjar cewa tsohon shugaban ya yi ritaya
  • Sai dai Kwamared Victor Amoko ya mayar da martanin cewa yana nan daram a matsayin shugaba domin bai yi ritaya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Rikici ya barke a kungiyar kwadago NLC reshen jihar Ondo yayin da mutane biyu ke ikirarin shugabancin ƙungiyar.

NLC reshen jihar Ondo ta dare gida biyu ne a daidai lokacin da Kwamared Victor Amoko da Kwamared Olapade Ademola suke ikirarin shugabanci.

Kara karanta wannan

Ganduje ya gamu da matsala, ɗan majalisa ya yi fatali da naɗin da aka masa a APC

Yan kwadago.
Kungiyar NLC ta shiga matsala, shugabanni biyu sun bayyana a Ondo Hoto: Nigeria Labour Congress HQ
Asali: Twitter

Yadda NLC ta dare gida 2 a Ondo

Daily Trust ta ce an zabi Ademola a matsayin shugaban kungiyar a wani taro na musamman da majalisar zartarwar NLC ta jihar (SEC) ta gudanar ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron da aka zaɓi Ademola ya samu halartar kungiyoyi 22 kuma mataimakin shugaban kungiyar NLC, Kwamared Busola Adewumi ne ya jagoranta.

Sai dai mambobin kungiyar malamai ta Najeriya NUT da kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi (NULGE) na Ondo sun kauracewa zaben da aka yi har Ademola ya yi nasara.

A cewar ƙungiyoyin ma'aikatan da suka zaɓi sabon shugaban NLC na Ondo, sun yi haka ne saboda tsohon shugaban ƙungiyar, Victor Amoko ya yi ritaya daga aiki.

Shugaban NLC na Ondo ya yi ritaya?

Da yake martani Amoko wanda mamba ne a kungiyar malamai NUT ya ce yana nan daram a matsayin shugaban kungiyar NLC ta Ondo saboda har yanzu yana kan aiki.

Kara karanta wannan

Ribas: Wani shugaban ƙaramar hukuma ya nada sababbin hadimai sama da 300

A rahoton This Day, Kwamared Amoko ya ce:

"Ban yi ritaya ba, gwamnan Ondo ya tsawaita wa'adin wasu ma'aikata (malamai) kuma ina cikinsu, sun ce ba zasu bari na ci gaba da zama a matsayin shugaban NLC ba.
"Har yanzu ina aiki kuma hakan ya sa na zama mamban NLC, sun tura wasiƙa ga NLC ta ƙasa amma babu wata amsa har yanzu, ina nan daram a shugabancin NLC."

Gwamnatin Tinubu ta shirya ƙara albashi

A wani rahoton kuma Gwamnatin tarayya karkashin Bola Ahmed Tinubu ta bayyana ƙwarin guiwar cewa za a warware batun sabon mafi karancin albashi nan da makon gobe.

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris da takwararsa ƙaramar ministan kwadago Nkeiruka Onyejeocha ne suka bayyana haka a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262