Gwamna Ya Faɗi Adadin Ɗaliban da Suka Mutu Yayin da Gini Ya Danne Mutum 200

Gwamna Ya Faɗi Adadin Ɗaliban da Suka Mutu Yayin da Gini Ya Danne Mutum 200

  • Gwamnatin jihar Filato ta ce ɓangaren da ya ruguje a makarantar sakandiren Saints Academy yana ɗauke da ɗalibai kusan 200
  • Kwamishinan yaɗa labarai da sadarwa na jihar, Musa Ashoms ne ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyara makarantar ranar Jumu'a
  • Makarantar ta rufta kan ɗalibai yayin da suke tsakiyar zana jarabawar karshen zango na uku a yankin ƙaramar hukumar Jos

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Plateau - Kimanin dalibai 200 ne suka makale a ginin makarantar da ya ruguje da safiyar Juma'a, 12 ga watan Yuli, 2024 a jihar Filato.

Kwamishinan yaɗa labarai da sadarwa na jihar Filato, Mista Musa Ashoms ne ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyara makarantar a Busa Buji da ke yankin Jos.

Kara karanta wannan

Ribas: Wani shugaban ƙaramar hukuma ya nada sababbin hadimai sama da 300

Gwamna Caleb Mutfwang.
Gwamnatin Filato ta ce kusan ɗalibai 200 gini ya danne a makaranta a Jos Hoto: Caleb Mutfwang
Asali: Facebook

Hukumar dillancin labarai (NAN) ta rahoto cewa makarantar sakandare ta Saints Academy da ke Jos ta ruguje yayin da dalibai ke tsaka da rubuta jarabawar zango na uku.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Filato ta tura tawaga makarantar

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa kwamishinan yaɗa labarai ya ziyarci makarantar da lamarin ya faru tare da rakiyar wasu kwamishinoni.

Da yake jawabi ga manema labarai, Mista Ashoms ya ce makarantar tana da ɗalibai 400 kuma kusan 200 ginin ya rufta kansu.

Kwamishinan ya ƙara da bayanin cewa bangaren makarantar da ya ruguje yana daukar dalibai kusan 200, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Gwamna Mutfwang ya roƙi likitoci

'Rushewar ginin ya yi sanadin rasa rayuka kuma yanzu haka ana ci gaba da kwashe ɗaliban da lamarin ya shafa zuwa asibiti, ba zamu iya tantance adadin da suka mutu ba a yanzu.

Kara karanta wannan

Jos: Ginin makaranta ya rufta kan ɗalibai suna tsakiyar zana jarabawa

"Ma'aikatan agaji suna ƙoƙari sosai wajen zaro ɗalibai daga ɓaraguzan ginin. Gwamna Caleb Mutfwang ya roƙi likitoci su tabbata sun ceto rayukan waɗanda suka tsira."
"Kada su tsaya neman a biya kudi kafin su duba ɗaliban saboda lamari ne na gaggawa."

- Musa Ashoms.

Gini ya rufta kan ƴan NYSC

A wani rahoton na daban kun ji cewa wasu mata masu hidimar kasa a sansanin NYSC dake Emure a jihar Ekiti sun tsallake rijiya da baya.

An ce suna tsaka da shirin yin wanka a safiyar Juma'a ne bangon bandakin ya rufta musu tare da danne su cikin kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262