Gwamnoni Za Su Yi Zama Kafin Ba Kananan Hukumomi Yanci, Za Su Tattauna Abu 1

Gwamnoni Za Su Yi Zama Kafin Ba Kananan Hukumomi Yanci, Za Su Tattauna Abu 1

  • Kungiyar gwamnonin Najeriya ta bayyana yadda ta dauki hukuncin kotun koli kan yancin ƙananan hukumomi
  • Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Kwara, Abdulrazaq Abdulrahman ne ya magantu a madadin gwamnonin
  • A makon nan ne kotun kolin Najeriya ta ba kanan hukumomin cin gashin kansu domin su rika sarrafa kuɗinsu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnonin Najeriya sun yi martani bayan kotun tarayya ta ba ƙananan hukumomi damar cin gashin kansu.

Kungiyar gwamnoni ta bayyana matsayarta tare da faɗin matakin da za ta dauka na gaba kan lamarin.

Gwamnonin jihohi
Gwamnoni sun yi matsaya kan hukunci kotun koli. Hoto: Abdul no Shaking
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan jihar Kwara, Abdulrazaq Abdulrahman ne ya magantu a madadin gwamnonin.

Kara karanta wannan

Kananan hukumomi: Tsohon gwamna ya soki hukuncin kotu, ya fadi illar haka ga Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnoni za su samu sauki

Gwamna Abdulrazaq Abdulrahman ya ce cire kananan hukumomi daga karkashinsu tamkar an sauke musu nauyi ne, rahoton Daily Post.

Abdulrazaq Abdulrahman ya ce lokuta da dama gwamnonin ne ke ɗaukar dawainiyar ƙananan hukumomi amma yanzu sun yasar da kwallon mangwaro.

Kananan hukumomi: Matsayar gwamnoni

Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya ya ce duk da ba su da wata matsala da hukuncin da kotu ta yi, za su zauna domin fahimtar abin da kotun ta yanke.

Gwamna Abdulrazaq Abdulrahman ya ce a ranar Laraba mai zuwa ne za su zauna domin kara fahimtar dokar da kuma dukan mataki na karshe.

Kwara ba ta da matsala da hukuncin

Duk da haka, gwamna Abdulrazaq Abdulrahman ya ce bai taba kudin kananan hukumomi a jiharsa.

Saboda haka wannan hukuncin ba zai jawo wata matsala a jihar ba kuma komai zai cigaba da tafiya daidai.

Kara karanta wannan

Tinubu ya dauki muhimmin alkawari bayan hukuncin kotun koli kan kananan hukumomi

Kananan hukumomi: Atiku ya magantu

A wani rahoton, kun ji cewa Alhaji Atiku Abubakar ya nuna farin ciki bisa hukuncin da kotun ƙolin Najeriya ta yanke na ƴantar da ƙananan hukumomi daga hannun gwamnoni 36.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ayyana hukuncin a matsayin wata babbar nasara ga dukkan ƴan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng