An Jefi Ali Ndume da Rashin Ladabi Ga Tinubu Saboda Ya Yi Magana Kan Yunwa

An Jefi Ali Ndume da Rashin Ladabi Ga Tinubu Saboda Ya Yi Magana Kan Yunwa

  • Fitacciyar kungiyar dalibai ta PSM ta yi martani mai zafi ga Sanata Ali Ndume kan bayanan da ya yi ga shugaba Bola Tinubu
  • Kungiyar PSM ta ce akwai cin fuska ga shugaban kasa Bola Tinubu da jami'yyar APC cikin abin da Sanata Ali Ndume ya fada
  • Sanata Ali Ndume ya nuna cewa shugaban kasa Bola Tinubu yana zagaye da mutanen da ba su bari ya gana da jami'ansa a kan lamuran kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kalaman Sanata Ali Ndume kan cewa ko da jami'an gwamnati da kyar suke samun ganin shugaban kasa sun tayar da kura.

Wata kungiyar dalibai ca ta yi martani ga Sanatan tana mai cewa babu gaskiya cikin kalaman da ya yi

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi sabon albashin da zai iya biyan ma'aikata, NLC ta dage kan N250,000

Ali Ndume
Kungiya ta gargadi Ali Ndume bayan magana kan Tinubu. Hoto: Sen. Ali Muhammad Ndume.
Asali: Facebook

Haka zalika jaridar Leadership ta ruwaito cewa kungiyar ta shawarci Ali Ndume kan abin da ya kamata ya mayar da hankali a kai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

PSM: 'Ba wanda yake juwa Tinubu'

Shugaban kungiyar PSM, Bestman Okereafor ya ce maganar cewa wasu ne ke juya Bola Tinubu ba gaskiya bace.

Bestman ya ce a matsayin Bola Tinubu na shugaban askarawan Najeriya, shi yake juya mulkinsa da kansa.

Ya kuma kara da cewa cikin maganar da Ali Ndume ya yi akwai rashin ladabi ga ofishin shugaban kasar Najeriya.

PSM ta ba Ndume shawara

Kungiyar PSM ta ce akwai bukatar Sanata Ndume ya koma gida jihar Borno domin magance matsalolinsu, rahoton Pulse Nigeria.

Ta ce nemo hanyar magance matsalolin tsaro musamman a mazabarsa ne babban abin da ya kamata ya mayar da hankali a kai.

Kara karanta wannan

Ana shirin zanga zanga, gwamnati ta dauki matakin gaggawa domin samar da abinci

A karshe, kungiyar ta yi kira ga Bola Tinubu kan ya kara kokari wajen gaggauta magance manyan matsalolin Najeriya.

Ali Ndume ya yi magana kan ECOWAS

A wani rahoton, kun ji cewa dan majalisar wakilan kungiyar hadin kan kasashen Afirka ta yamma, Sanata Ali Ndume ya ce kasashen da suka fita daga ECOWAS za su dawo.

Sanata Ali Ndume ya bayyana haka ne yayin hira da manema labarai bayan wani taron majalisar kungiyar da ya gudana a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng