Kananan Hukumomi: Tsohon Gwamna Ya Soki Hukuncin Kotu, Ya Fadi Illar Haka Ga Najeriya

Kananan Hukumomi: Tsohon Gwamna Ya Soki Hukuncin Kotu, Ya Fadi Illar Haka Ga Najeriya

  • Tsohon gwamnan jihar Delta ta caccaki hukuncin Kotun Koli kan shari'ar Gwamnatin Tarayya da kuma gwamnonin jihohi 36
  • James Ibori ya ce kwata-kwata hukuncin bai yi ba kuma koma-baya ne ga kasar wanda ya saba dokokin kundin tsarin mulki
  • Wannan martani na zuwa ne kwana ɗaya bayan Kotun Koli ta raba gardama kan shari'ar da ake yi game da ƴancin ƙananan hukumomi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Delta - Tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori ya yi martani bayan hukuncin kotu kan ƙananan hukumomi.

Tsohon gwamnan ya bayyana hukuncin a matsayin koma-baya a tsarin mulkin kasa bai daya.

Tsohon gwamna caccaki hukuncin kotu kan kananan hukumomi
Tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori ya soki hukunci kan ƴancin ƙananan hukumomi. Hoto: James Ibori.
Asali: Facebook

Kananan hukumomi: James Ibori ya magantu

Kara karanta wannan

Tinubu ya dauki muhimmin alkawari bayan hukuncin kotun koli kan kananan hukumomi

Ibori ya bayyana haka ne a shafinsa na X a jiya Alhamis 11 ga watan Yulin 2024 bayan yanke hukuncin Kotun Koli.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya nuna damuwa kan hukuncin inda ya kawo wasu hujjoji a kundin tsarin mulki da ya ce sun saba ka'idar doka.

Har ila yau, ya kawo hujjoji daga sashe 162 na kundin tsarin mulkin Najeriya inda ya ce an saɓa ka'idoji da dama kan yanke hukuncin.

Ibori ya ce hukuncin ya saba doka

"Duk kudaden da ke asusun Gwamnatin Tarayya za ta raba su gare ta da jihohi da kuma kananan hukumomi."
"Kowace jiha za ta yi amfani da asusun bai daya da ake kira 'State Joint Local Government Account' da za a saki kudaden har da na kananan hukumomi."
"Gwamnatin Tarayya ba ta da hurumin shiga tsakanin gwamnoni da gudanar da kananan hukumomi."

Kara karanta wannan

Kananan hukumomi: Atiku ya mayar da martani kan hukuncin kotun ƙolin Najeriya

"Matakan gwamnati biyu ne kacal a tsarin mulkin Tarayya da ake amfani da shi a Najeriya."

- James Ibori

Kotu ta yi hukunci kan ƙananan hukumomi

Kun ji cewa Kotun Koli ta raba gardama kan shari'ar Gwamnatin Tarayya da kuma gwamnonin jihohi 36 a Najeriya.

Kotun ta soki tsarin da ake wanda gwamnoni ke gudanar da kudaden ƙananan hukumominsu ba tare da ƴanci ba.

Ta umarci Gwamnatin Tarayya ta fara biyan ƙananan hukumomi daga asusunta kamar yadda take biyan jihohi a yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.