Ibadan: Sabon Sarki Ya Kafa Tarihi, An Naɗa Masa Rawanin Sarauta Mai Ƙima a Najeriya

Ibadan: Sabon Sarki Ya Kafa Tarihi, An Naɗa Masa Rawanin Sarauta Mai Ƙima a Najeriya

  • Oba Owolabi Akinloye Olakulehin ya zama sabon Olubadan na ƙasar Ibadan bayan naɗa masa rawani yau Jumu'a, 13 ga watan Yuli, 2024
  • Sabon sarkin mai sheksru 86 a duniya ya zama Olubadan na 43 a tarihin masarautar Ibadanland bayan naɗin da Gwamna Makinde ya masa
  • Ana tsammanin gwamnan zai mika masa sandar mulki da takardar kama aiki a babban ɗakin taron Mapo da ke birnin Ibadan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Oyo - Bayan amincewar Gwamna Seyi Makinde a makonnin baya, a yau Jumu'a, 12 ga watan Yuli, 2024, Oba Owolabi Akinloye Olakulehin ya kafa tarihin zama Olubadan na 43.

Oba Olakulehin mai shekara 85 ya zama sabon sarkin ƙasar Ibadan, sarauta mai ƙima da daraja a jihar Oyo wadda aka fi sani da Olubadan na Ibadanland.

Kara karanta wannan

Ribas: Wani shugaban ƙaramar hukuma ya nada sababbin hadimai sama da 300

Oba Olakulehin na Ibadanland.
An naɗawa Olakulehin rawanin Sarautar Olubadan a jihar Oyo Hoto: Francis Owolabi
Asali: Twitter

Kamar yadda Leadership ta ruwaito, an naɗawa sabon sarkin rawani a harabar gidan Labosinde, dangin da ke da alhakin naɗa rawani ga duk wanda aka naɗa bisa al'ada.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanai sun nuna cewa jim kaɗan bayan kammala naɗa masa rawanin sarautar, Oba Olakuleyin ya koma fadar Ile Osemeji da ke unguwar Oja Oba a birnin Ibadan.

Ana ganin Ile Osemeji ita ce fadar sarki faɗi daraja kuma ana wa fadar laƙabin wurin tsara makomar Ibadan, kamar yadda jaridar The Nation ta tattaro.

Gwamna Makinde zai mika sandar girma

Ana sa ran nam ba da jimawa ba Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo zai miƙa sandar girma da takardar kama aiki ga sabon sarkin Ibadan.

Rahotanni sun nuna cewa mai girma gwamna zai miƙa dukkan kayayyakin naɗin sabon Olubadan ɗin a babban ɗakin taron Mopa da ke birnin Ibadan yau Jumu'a.

Kara karanta wannan

Jos: Ginin makaranta ya rufta kan ɗalibai suna tsakiyar zana jarabawa

Ɗan majalisar tarayya ya rasu

A wani rahoton kuma Majalisar Tarayya a Najeriya ta sake shiga jimami bayan rasuwar wani mambanta daga jihar Oyo a Kudancin kasar.

Marigayin mai suna Hon. Musiliu Olaide Akinremi ya kasance mamban Majalisar karo na biyu da ke wakiltar mazabar Ibadan ta Arewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262