Jos: Ginin Makaranta Ya Rufta Kan Ɗalibai Suna Tsakiyar Zana Jarabawa
- Ginin wata makaranta ya rushe kan ɗalibai da ke tsakiyar rubuta jarabawa a Busa Buji da ke ƙaramar hukumar Jos a jihar Filato
- Rahotanni sun bayyana cewa iyayen yara sun garzaya wurin suna kukan neman agaji kuma tuni jami'an tsaro suka dura makarantar
- Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar yau Jumu'a, 12 ga watan Yuli, 2024, yanzu haka an fara kokarin zakulo ɗaliban da ginin ya danne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jos, jihar Plateau - Rahotannin da muka samu sun nuna cewa yanzu haka dalibai da yawa sun makale a wata makaranta da ta rufta ana tsakiyar jarabawa a jihar Filato.
Lamarin ya faru ne a wata makaranta da ke unguwar Busa Buji a ƙaramar hukumar Jos ta jihar Filato a shiyyar Arewa ta Tsakiya.
A cewar shaidun gani da ido, ginin makarantar Saint Academy ya fado ne da misalin karfe 11 na safiyar yau Juma’a, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ganau sun bayyana cewa ginin ya danne ɗalibai da dama waɗanda ke zana jarabawa a makarantar.
An tattaro cewa bayan labarin rushewar ginin makarantar ya bazu a yankin, iyayen yara sun garzaya makaranta cikin tashin hankali suna kuka neman a ceto ƴaƴansu.
Jami'an tsaro sun kai ɗauki
Legit Hausa ta fahimci cewa yanzu haka an fara aikin ceto ɗaliban kuma jami'an tsaro da suka haɗa da sojoji da ƴan sanda sun isa wurin.
Haka nan kuma wata babbar mota da ta nufi wurin da ibtila'in ya afku domin kai agaji ta maƙale a taɓo sakamakon ruwan saman da aka yi.
Jos: Ana fargabar ɗalibai sun mutu
Wasu rahotanni sun yi ikirarin cewa an rasa rayuka sakamakon kifewar ginin makarantar amma a halin yanzu bamu da tabbacin faruwar hakan.
Kawo yanzu an yi nasarar ceto ɗaliban da ginin ya danne kuma tuni aka ɗauke su zuwa asibiti domin kula da lafiyarsu, rahoton Premium Times.
Babban limamin Jos ya rasu
A wani rahoton kun ji cewa Babban limamin masallacin Juma'a da ke birnin Jos a jihar Plateau, Sheikh Lawal Adam Abubakar ya rasu.
Marigayin ya riga mu gidan gaskiya ne a ranar Alhamis da ta gabata 11 ga watan Yulin 2024 a asibitin Jos yana da shekaru 80 a duniya.
Asali: Legit.ng