Jami'an DSS Sun Kai Samame Gidan Wani da Ake Zargi da Alaƙa da Ƴan Bindiga

Jami'an DSS Sun Kai Samame Gidan Wani da Ake Zargi da Alaƙa da Ƴan Bindiga

  • Dakarun hukumar DSS sun kai samame gidan wani ɗan adaidaita sahu da ake zargin yana da alaƙa da ƴan bindiga a jihar Neja
  • Rahotanni sun bayyana cewa jami'an tsaron sun kwato makamai da kuɗaɗe ciki harda Daloli a gidan mutumin ranar Laraba da ta gabata
  • Jami'in hulɗa na jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Neja ya ce ba su da masaniyar samamen da aka kai kwanan nan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Niger - Jami’an hukumar ‘yan sandan farin kaya (DSS) sun kai samame gidan wani da ake kyautata zaton ‘dan bindiga ne a unguwar Gbeganu da ke gefen birnin Minna a jihar Neja.

Jam'an tsaron sun kai wannan samamen da tsakar rana a ranar Laraba da ta shuɗe kuma lamarin ya haifar da fargaba a zuƙatan mazauna yankin.

Kara karanta wannan

Jos: Ginin makaranta ya rufta kan ɗalibai suna tsakiyar zana jarabawa

Jami'an DSS.
Jami'an DSS sun kai samame gidan wani mutumi da ake zargi da hannu a ta'addanci Hoto: DSS
Asali: Twitter

Wasu majiyoyin sun ce wannan shi ne samame na uku cikin kasa da shekaru hudu a yankunan da ke makwabtaka da Nkangbe da Gbeganu duk a karamar hukumar Bosso.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, jami'an DSS sun farmaki gidan mutumin ne saboda suna zargin shi ne ma'ajiyin wata ƙungiyar ƴan ta'adda.

DSS ta ƙwato makamai da Daloli

Duk da babu cikakken bayani kan irin makaman da jami'an DSS suka bankaɗo a gidan amma bayanai sun nuna an kwato abubuwa masu haɗari a hannunsa.

Mazauna unguwar sun shaidawa manema labarai cewa dakarun DSS sun ƙwato maƙudan kudi ciki harda Dalolin Amurka a lokacin samamen.

A ruwayar Sahara Reporters, wanda ake zargin direban adaidaita sahu ne gabannin yanzu da alamu suka nuna yana da alaƙa ɗa ayyukan ƴan bindiga.

Kara karanta wannan

Yobe: 'Yan sanda sun cafke basarake bisa zargin hannu a kisan wani bawan Allah

Yayin da aka tuntuɓe shi, kakakin rundunar ’yan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun ya bayyana cewa ba su da wani bayani dangane da samamen da DSS ta kai kwanan nan.

An kashe mataimakin kwamandan soji

A wani rahoton kun ji cewa jami'in gudanarwa a rundunar sojojin Operation Save Haven, Christopher Luka ya rasa ransa a jihar Filato da ke Arewa ta Tsakiya.

An tattaro cewa jami'in hukumar shige da ficen wanda ke aiki da rundunar ya mutu ne lokacin da ya jagoranci sojoji domin kwato shanu a Barkin Ladi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262