An Fadi Biliyoyin da 'Yan Najeriya Suka Bayar Na Cin Hanci ga Jami'an Gwamnati a 2023

An Fadi Biliyoyin da 'Yan Najeriya Suka Bayar Na Cin Hanci ga Jami'an Gwamnati a 2023

  • Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta bankado biliyoyin kudin da 'yan Najeriya su ka bayar a matsayin cin hanci
  • Kudin da yawansu ya kai Naira Biliyan 721, an bayar da su ne lakadan a wurare daban daban a shekarar 2023
  • Wadanda ke kan gaba wajen karbar na goron su ne jami'an lafiya, sai wasu jami'an gwamnati a tashoshi daban -daban

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Abuja- Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta bankado yadda 'yan Najeriya su ka kashe biliyoyin Naira a matsayin cin hanci ga jami'an gwamnati. Hukumar ta gano cewa akalla an bawa jami'an gwamnati Naira Biliyan 721 a matsayin cin hanci lakadan.

Kara karanta wannan

Fashin magarkama: 'Yan Boko Haram sama da 100 sun tsere daga gidan yarin Nijar

Bribe
Yan Najeriya sun bayar da cin hancin N721 a 2023 Hoto: PM Images
Asali: Getty Images

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa an tattaro wannan adadi ne a cikin shekarar 2023 kawai.

Cin hanci: An raina kokarin hukumomi

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa hukumar NBS ta gano 95% na cin hancin da aka bayar a 2023 na kudi ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton na NBS mai taken "Cin hanci a Najeriya: Yadda lamurra ke wakana" ya gano cewa 'yan kasar nan ba sa ganin tasirin hukumomin yaki da rashawa.

"A shekarar 2023, an biya 35% na cin hanci a ofishin jami'an gwamnati, kaso 36% kuma a wajen ofisoshin."
"11% na cin hancin an biya ne a gidajen masu jami'an, an bayar da 7% na cin hanci a wuraren shakatawa kamar gidan cin abinci, shaguna da tashoshi."

- Rahoton NBS

A cewar rahoton, jami'an lafiya su ne kan gaba wajen karbar cin hanci da 30% a shekarar 2023, sai jami'an gwamnati a tashoshin jama'a su ka take masu baya da 24%.

Kara karanta wannan

Kananan hukumomi: "Yanzu jama'a za su sharbi romon dimokuradiyya," APC

Jami'an 'yan sandan kasar nan su ne na uku a karbar cin hanci cikin shekarar 2023 da 20%.

"An nemi cin hanci a wajenmu," Binance

A baya mun ruwaito shugaban kamfanin hada-hadar kirifto na Binace, Richard Teng ya zargi jami'an gwamnatin kasar nan da neman su bayar da cin hanci.

Mista Teng ya ce an nemi su bayar da wani abu domin kawar da tuhume-tuhumen da gwamnatin Najeriya ke yiwa kamfaninsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.