Ana Fargabar Tsige Sarkin Musulmi Bayan Sabuwar Doka, an Gargadi Gwamna
- Kungiyoyin hadin kan Musulmi a Najeriya sun tura sabon sako ga gwamnatin jihar Sokoto bayan kafa sababbin dokokin masarautu
- Hakan na zuwa ne bayan da aka cigaba da samun fargaba kan zargin yunkurin tsige sarkin Musulmi da gwamnatin jihar ke yi
- A yanzu haka dai majalisar dokokin jihar Sokoto ta zartar da dokokin da suka yi kwaskwarima ga harkar masarautu a jihar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto - Gamayyar kungiyoyin Musulmi a Najeriya sun fusata biyo bayan yin kwaskwarima ga dokokin masarautu a Sokoto.
Kungiyoyin sun nuna fargaba kan cewa hakan zai rage martabar Sarkin Musulmi da kuma kimar Musulunci.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa kimanin kungiyoyin Musulmi 33 ne suka gargadi gwamnatin Sokoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me ya kamata gwamnan Sokoto ya yi?
Gamayyar kungiyoyin Musulmi sun ce abin da ya kamata gwamnan Sokoto ya yi shi ne karfafa mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III.
Kungiyoyin sun ce dukkan matakin da zai kawo karfafa masarautar Sokoto da samar da ayyukan cigaba su ya kamata gwamna Ahmad Aliyu ya yi.
Sarkin Musulmi na bukatar kariya
Har ila yau kungiyoyin sun ce akwai bukatar gwamna Ahmad Aliyu ya samar da dokar da za ta ba Sultan kariya, rahoton Vanguard.
Ta ce yin haka zai sa tarihi ya cigaba da tunawa da shi a matsayin wanda ya kawo cigaba da mutunta addinin Musulunci a Sokoto.
Kokarin da Tinubu zai yi
Haka zalika kungiyoyin sun ce akwai bukatar shugaba Bola Tinubu ya saka baki wajen ganin ba a samu wata matsala kan Sarkin Musulmi ba.
Kungiyoyin sun fadi haka ne saboda cewa Sarkin Musulmi jagora ne na al'ummar Musulmi a Najeriya baki daya.
Sarkin Musulmi ya magantu kan halin kunci
A wani rahoton, kun ji cewa mai alfarma Sarkin Musulmi ya yi magana kan halin ƙunci da tsadar rayuwa da ƴan Najeriya suka tsinci kansu a ciki a wannan lokacin.
Alhaji Sa'ad Abubakar III ya bayyana cewa kaucewa Allah da aka yi shi ne babban dalilin da ya sanya aka shiga cikin wannan halin
Asali: Legit.ng