Kano: Kotu ta yi Fatali da Bukatar 'Chuchu' da ake Zargi da Kisan Nafi'u
- Babbar kotun jihar Kano ta dauki matsaya kan bukatar lauyoyin Hafsat Surajo da ake zargi da kashe yaron gidanta
- Ana zargin Hafsat da aka fi sani da Chuchu da caccakawa Nafi'u Hafiz Gorondo wuka a sassan jikinsa
- Amma idan an je kotu ba ta magana, lamarin da ya sa lauyoyinta neman a gwada lafiyar kwakwalwarta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano- Babbar kotun jihar Kano dake zaman ta a sakatariyar Audu Bako ta dauki mataki kan shari'ar Hafsat Surajo da aka fi sani da 'Chuchu'. Ana tuhumar Chuchu da laifin hallaka yaron gidanta, Nafi'u Hafiz Gorondo ta hanyar daddaba masa wuka a sassan jikinsa.
Daily Trust ta wallafa cewa a zaman kotu na yau, Mai Shari'a Faruk Lawan, ya yi watsi da bukatar lauyoyin Chuchu.
Menene bukatar lauyoyin Chuchu?
A zaman kotu da aka yi kan shari'ar kisan Nafi'u a Kano, lauyoyin wacce ake zargi da aikata kisan sun nemi a kai Chuchu asibiti.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A zaman kotun da ake ta yi, Chuchu ta yi gum da bakinta, ba ta cewa komai wannan ya sa lauyanta ya nemi lallai a kai da asibiti domin gwajin kwakwalwa.
Sai dai Mai Shari'a Faruk Lawan ya ki amincewa, inda ya ce bai gamsu da dalilan da aka bayar na duba lafiyarta ba, domin ta na magana da mijinta da sauran mutane.
Lauyan mai kara, Aisha Salisu ta nemi a basu damar gabatar da shaidu, kuma mai shari'a dage ci gaba da sauraron shari'ar zuwa ranakun 13, 14 da 15 Yuli.
Ana zargin Hafsat Surajo da manyan laifuka guda biyu, sun hada da kisan kai da yunkurin kashe kanta.
An mayar da mijin Chuchu gidan yari
A wani labarin kun ji cewa kotu ta bayar da umarnin tesa keyar Dayyabu mijin Chuchu zuwa gidan yari bisa zargin kashe Nafi'u.
Ana zargin Hafsat Surajo, mijinta Dayyabu Abdullahi, Adamu Muhammad da Nasidi Muhammad da laifin kashe yaron gidanta Chuchu, Nafi'u Hafiz.
Asali: Legit.ng