Ana Murnar Janye Haraji, Gwamnati ta Gindaya Sharadi Kan Farashin Kaya
- Gwamnatin tarayya ta ce za ta kayyade farashin abincin da za a rika shigowa da shi kasar nan idan an janye haraji
- Ministan noma da samar da abinci, Abubakar Kyari ne ya bayyana haka inda yace gwamnati za ta dauki matakin kawar da yunwa
- Ministan ya ce gwamnati za ta dauki matakan kawar da yunwa domin tabbatar da cewa yan kasa sun samu sauki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Abuja- Yayin da ake murna kan janye haraji kan wasu nau'in abinci, gwamnatin tarayya ta ce akwai sharadi kan farashin abinci. Matakin na zuwa bayan gwamnatin ta bayyana cewa za a janye harajin shinkafa, masara da alkama da wasu nau'in abinci.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Ministan noma da samar da abinci, Abubakar Kyari ya ce gwamnati za ta tabbatar da karya farashin abinci.
"Za a magance yunwa": Minista
Ministan noma da samar da abinci, Abubakar Kyari ya bayyana cewa ana daukar matakin kawar da yunwa a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Ministan ya ce za a dauki matakin tabbatar da cewa an kayyade farashin abincin da za a shigo da shi.
Ya ce tunda gwamnati ta amince da janye harajin wasu nau'in abinci na kwanaki, za a sanya idanu wajen tabbatar da farashin da za a sayar da abincin a kasuwanni.
Ministan ya nanata cewa gwamnati za ta shigo da tan 250,000 na masara da alkama, a yunkurin tabbatar da cewa an daina kwana da yunwa a kasar nan.
Daga sauran matakan da ya ce za a dauka akwai tallafawa kananan manoma wajen noman damuna da na rani.
"Farashin abinci ba zai sauko ba:" Yan kasuwa
A baya kun ji cewa kungiyar yan kasuwa ta bayyana cewa dakatar da harajin abincin ba zai kawo saukin farashi ba. Shugaban kungiyar 'yan kasuwa a Kano, Dr. AbdulAziz Bature ya ce akwai hanyoyin da ya kamata a bi wajen kawar da yunwa.
Asali: Legit.ng