Gwamnatin Borno Ta Dauki Mataki Kan Tubabbun 'Yan Boko Haram 8,940

Gwamnatin Borno Ta Dauki Mataki Kan Tubabbun 'Yan Boko Haram 8,940

  • Gwamnatin jihar Borno ta yaye tubabbun ƴan Boko Haram 560 waɗanda za a mayar da su cikin al'umma bayan an gama ba su horo da koya musu sana'o'i
  • Wannan na cikin tsarin da gwamnatin take da shi na mayar da waɗanda suka tuba zuwa cikin al'umma, inda ya zuwa yanzu ta mayar da mutum 8,940
  • Kwamishinan yaɗa labarai na jihar ya ce bincike ya nuna cewa waɗanda aka mayar cikin al'umma ba su karya doka kuma ba su komawa cikin daji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Gwamnatin jihar Borno ta bayyana cewa ta samu nasarar dawo da tubabbun ƴan Boko Haram 8,490 cikin al'umma ta hanyar tsarin 'Borno Model'.

Maƙasudin shirin ba tubabbun ƴan ta'adddan ilmi da sana'a domin samun damar sake shiga cikin al'umma.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan yiwa 'yan NYSC karin alawus

Tubabbun 'yan Boko Haram sun koma cikin al'umma a Borno
Gwamnatin Borno ta mayar da tubabbun 'yan Boko Haram cikin al'umma Hoto: Professor Babagana Umara Zulum
Asali: Facebook

Tubabbun ƴan ta'addan ba su da haɗari

Kwamishinan yaɗa labarai da tsaro na cikin gida, Farfesa Usman Tar, ya shaidawa jaridar Daily Trust a wani taron rantsuwa da aka shiryawa tubabbun ƴan ta’adda 560 a Maiduguri a ranar Laraba, cewa su ba su da haɗari kuma yara ne ƙanana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce sojoji da sauran jami’an tsaro sun tantance su tare da shugabannin gargajiya na ƙauyukansu daban-daban.

Ya ce shirin ya samu nasara kuma sun gudanar da bincike wanda ya nuna cewa wadanda aka dawo da su cikin al’umma ba su taɓa karya wata doka ba, haka kuma ba su komawa daji.

"A cikin shekaru uku da suka wuce, mun kafa tsarin 'Borno Model' domin mayar da tubabbun ƴan ta'adda cikin al'umma."
"A yau muna yaye ƙarin mutum 560 waɗanda ba su da haɗari kuma yara ne ƙanana. An basu horo akan gyaran waya, kanikanci, aikin kafinta da duk wasu sana'o'i."

Kara karanta wannan

Katsina: 'Yan bindiga sun turo saƙon bidiyon mutanen da suka sace a Maidabino

- Farfesa Usman Tar

Tubabbun ƴan ta'adda 8,940 sun koma cikin al'umma

Mai ba gwamnan Borno shawara kan harkokin tsaro, Birgediya Janar Abdullahi Ishaq (mai ritaya), ya bayyana cewa ya zuwa yanzu sun mayar da tubabbun ƴan ta'adda 8,490 waɗanda da yawa daga cikinsu ƙananan yara ne cikin al'umma.

"Mun mayar da mutum 8,490 waɗanda da yawa yara ne ƙanana. A baya mun mayar da mutum 7,930 yanzu kuma ga mutum 560, da yawa daga cikinsu ba su shekara 10 ba lokacin da ƴan ta'addan suka tafi da su da ƙarfin tsiya."

- Birgediya Janar Abdullahi Ishaq

Amfanin tubabbun ƴan Boko Haram

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Yobe ta bayyana cewa tubabbun ƴan Boko Haram na taimakawa wajen yaƙi da ta’addanci a jihar.

Gwamnatin ta ce tubabbun ƴan ta'addan na Boko Haram na taka muhimmiyar rawar gani wajen kawo ƙarshen ayyukan ƴan ta'adda a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng