Plateau: An Kashe Mataimakin Kwamandan Rundunar Sojojin Najeriya

Plateau: An Kashe Mataimakin Kwamandan Rundunar Sojojin Najeriya

  • Jami'in gudanarwa a rundunar sojojin Operation Save Haven, Christopher Luka ya rasa ransa a jihar Filato da ke Arewa ta Tsakiya
  • An tattaro cewa jami'in hukumar shige da ficen wanda ke aiki da rundunar ya mutu ne lokacin da ya jagoranci sojoji domin kwato shanu a Barkin Ladi
  • Har kawo yanzu mai magana da yawun rundunar Safe Haven, Manjo Samson Zhakom bai fitar da sanarwa a hukumance kan lamarin ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Plateau - Wani babban jami'in hukumar shige da fice da ke aiki da rundunar haɗin guiwa ta Operation Save Haven, Christopher Luka ya rasa rayuwarsa a Filato.

Rahotanni sun nuna cewa an kashe Luka, wanda ke aiki a matsayin jami'in gudanarwa na sashi na 4 a rundunar ranar Laraba a ƙaramar hukumar Barikin Ladi.

Kara karanta wannan

Yobe: 'Yan sanda sun cafke basarake bisa zargin hannu a kisan wani bawan Allah

Sojojin Najeriya.
Wasu ƴan bindiga sun hallaka mataimakin kwamandan rundunar sojoji a Plateau Hoto: Nigerian Army
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kashe babban jami'in a yankin ƙauyen Fan da ke ƙaramar hukumar Barikin Ladi a daren ranar Laraba, 10 ga watan Yuli.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rundunar haɗin guiwa ta Operation Save Haven ta ƙunshi dakarun sojoji, jami'an shige da fice, ƴan sanda, jami'an tsaron fararen hula (NSCDC), da kwastam.

Wannan runduna ita ke da alhakin wanzar da zaman lafiya a jihar Filato kuma bayanai sun nuna cewa Christopher Luka na aiki da sashi na huɗu na rundunar a matsayin mataimakin kwamanda.

Yadda aka kashe Christopher Luka

Wasu majiyoyi daga Barikin Ladi sun nuna cewa an kashe babban jami'in ne lokacin da ya jagoranci dakarun sojoji domin ceto wasu shanu da aka sace a yankin.

An tattaro cewa ɓarayi sun sace shanu 92 amma an yi nasarar ƙwato 52 daga ciki sakamakon namijin ƙoƙarin marigayi kwamanda, rahoton Naija News.

Kara karanta wannan

An samu raunuka bayan makiyaya sun farmaki jami'an tsaro

Rahoto ya nuna cewa ƴan bindiga sun farmaki jami'an tsaron a lokacin da suke ƙoƙarin ƙwato sauran shanu 40.

Legit Hausa ta fahimci cewa tuni dakaru suka mamaye yankin bayan kisan mataimakin kwamandan ranar Laraba.

Har kawo yanzu da muke haɗa wannan rahoton kakakin rundunar Manjo Samson Zhakom bai fitar da sanarwa a hukumance kan lamarin ba.

An kama basarake da hannu a kisa

A wani rahoton jami'an ƴan sanda sun kama wani dagaci bisa zargin hannu a kisan direban motar tarakta a jihar Yobe da ke Arewa maso Gabas.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, DSP Dungus Abdulkareem ya ce basaraken ya haɗa matasa suka je gona suka aikata kisan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262