El Rufai Ya Sake Caccakar Uba Sani, Ya Fadi Makarkashiyar da Aka Yi Masa

El Rufai Ya Sake Caccakar Uba Sani, Ya Fadi Makarkashiyar da Aka Yi Masa

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya sake caccakar Gwamna Uba Sani na jihar wanda ya gaje shi
  • El-Rufai ya zargi gwamnan da ƙoƙarin ɓata masa suna da gwamnatinsa kan zargin karkatar da N423bn da ake yi masa
  • Wasu tsofaffin kwamishinonin jihar ne suka faɗi hakan a madadin El-Rufai inda suka bayyana rahoton binciken a matsayin wanda yake cike da ƙarya da ƙarairayi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya sake caccakar magajinsa, Gwamna Uba Sani na jihar.

El-Rufai ya caccaki Uba Sani ne bisa zargin haɗa ƙarya da ƙarairayi wajen zargin gwamnatinsa da karkatar da maƙudan kuɗaɗen da suka kai N423,115,028,072.88.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya nemi wata alfarma wajen mutanen Katsina kan matsalar tsaro

El-Rufai ya caccaki Uba Sani
El-Rufai ya caccaki Gwamna Uba Sani Hoto: @ubasanius, @elrufai
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan ya yi magana ne ta bakin tsofaffin kwamishinoninsa a wani taron manema labarai a birnin tarayya Abuja a ranar Talata, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana son ɓata sunan El-Rufai a Kaduna

El-Rufai ya yi watsi da rahoton kwamitin da aka kafa domin bincikensa, inda ya ce rahoton ba shi da makama ba, kuma da gangan Uba Sani da tawagarsa suka shirya shi domin ɓata masa suna da gwamnatinsa.

A cewar tsofaffin kwamishinonin, zargin da gwamnatin ke yi na wawure N423,115,028,072.88 daga ranar 29 ga watan Mayun 2015 zuwa ranar 29 ga watan Mayun 2023 abin dariya ne, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Sun bayyana cewa rahoton bai nuna daga inda aka kwashe kuɗaɗen ba da yadda aka kwashe su da kuma wanda ya kwashe kuɗaɗen.

Tsofaffin kwamishionin sun bayyana cewa rahoton bai nuna ta yadda suka samo wannan adadin ba, yadda suka yanke shawarar cewa an sace kuɗaɗen da yadda aka yi satar kuma daga wane asusu zuwa wane asusu.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fusata kan jami'an gwamnati da suka karkatar da kudaden ma'aikata, ya ba su umarni

Tsofaffin kwamishinonin sun yi watsi da rahoton na Uba Sani tare da zarginsa da ɓata sunan El-Rufai da ƴan tawagarsa duk da cewa ayyukan da yake nunawa yanzu a matsayin na shi, an yi su ne da basussukan da tsohuwar gwamnatin ta ci yo.

Kotu ta fara zama a shari'ar El-Rufai

A wani labarin kuma, kun ji cewa babbar kotun tarayya dake da zama a Kaduna, ta dage sauraron ƙarar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya shigar zuwa 17 ga Yulin 2024.

Nasir El-Rufai ne ya maka majalisar jihar Kaduna da Antoni Janar na jihar a gaban kotun inda yake kalubalantar rahoton kwamitin majalisar da ya nuna cewa ya saci kudin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng