Hukumar NERC Ta Lissafa Kayan Lantarki da Ya Kamata a Rika Ba Yan Najeriya Kyauta

Hukumar NERC Ta Lissafa Kayan Lantarki da Ya Kamata a Rika Ba Yan Najeriya Kyauta

  • Hukuma mai kula da wutar lantarki a Najeriya (NERC) ta ja kunnen yan Najeriya kan biyan kudi domin mallakar wasu kayan lantarki
  • NERC ta bayyana cewa akwai kayan rarraba wutar lantarki da bai kamata ace yan Najeriya suna saye da kuɗinsu ba kwata kwata
  • Har ila yau, hukumar ta bayyana wadanda ya rataya a wuyansu domin ganin yan Najeriya sun samu kayan rarraba wutar lantarki a kyauta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Hukuma mai kula da wutar lantarki a Nigeriya (NERC) ta yi karin haske kan sayen kayayyakin rarraba wuta.

Hukumar NERC ta ce sam bai kamata dan Najeriya ya rika sayen kayayyakin rarraba wuta da kudinsa ba.

Kara karanta wannan

Auren jinsi: Yadda kururuwar mutanen Kano ya dakile yunkurin kungiyar LGBTQ

Randar wutar lantarki
Hukumar NERC ta bukaci mutane su daina sayen kayan rarraba wuta. Hoto: Robert Brook
Asali: Getty Images

Legit ta tatttaro bayanan ne a cikin wani sakon haɗe da bidiyo da hukumar NERC ta wallafa a shafinta na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ya kamata a samar kyauta?

Hukumar NERC ta bayyana cewa kayan rarraba wuta kamar trasifoma, wayar wuta ba sandunan kafa wayar wuta ba a kan yan Najeriya suke ba.

NERC ta ce kada yan Najeriya su yarda a tilasta musu sayen wadannan abubuwan idan suka lalace, rahoton Tribune.

Wa zai samar da kayayyakin?

Hukumar NERC ta tabbatar da cewa hakkin kamfanonin rarraba wutar lantarki ne su samar da su ga al'umma.

Saboda haka ya kamata da zarar an samu matsala dangane da kayayyakin ayi gaggawar sanar da kamfanonin rarraba wuta domin ɗaukan mataki.

Ya za a yi idan ba su kawo su ba?

Har ila yau, hukumar NERC ta bayyana cewa idan kamfanonin rarraba wutar lantarki ba su samar da kayayyakin a kan lokaci ba a gaggauta sanar da ita.

Kara karanta wannan

CBN ya yi albishirin rage kudin ruwa, watakila a samu sauki bayan korafin Dangote

A kan haka ne ma NERC ta samar da lambar wayar kiran gaggawa da imel da za a tura mata korafi kan lamarin.

An dawo magana kan wutar Mambila

A wani rahoton, kun ji cewa majalisar dattawan Najeriya ta dawo da magana kan wutar Mambila da aka kashe makudan kudi domin samar da ita a shekarun baya.

A zaman majalisar na makon da ya wuce aka tattauna kan yadda za a cigaba da aikin da kuma binciken yadda kuɗin aikin ya salwanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng