'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Ji Wuta, Sun Mika Wuya Ga Dakarun Sojoji

'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Ji Wuta, Sun Mika Wuya Ga Dakarun Sojoji

  • Wasu daga cikin mayaƙan ƙungiyar ta'addanci ta Boko Haram sun miƙa wuya ga sojoji a yankin tafkin Chadi
  • Ƴan ta'addan tare da iyalansu 69 sun miƙa wuya ne ga dakarun rundunar haɗi gwiwa ta ƙasa da ƙasa (MNTJF)
  • Miƙa wuyar da ƴan ta'addan suka yi na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun sojojin ke ƙara matsa ƙaimi wajen kawo ƙarshen ayyukansu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jamhuriyar Chadi - Ƴan ta'addan Boko Haram da iyalansu sun miƙa wuya ga dakarun rundunar haɗin gwiwa ta ƙasa da ƙasa (MNJTF).

Ƴan ta'addan da suka miƙa wuya su 69 tare da iyalansu an miƙa su zuwa hedkwatar rundunar ta MNJTF da ke birnin N'jamena na Jamhuriyar Chadi.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sanye da kayan mata sun sace mutane masu yawa a Katsina

'Yan ta'addan Boko Haram sun mika wuya a hannun sojoji
'Yan ta'addan Boko Haram sun ajiye makamansu a tafkin Chadi Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Ƴan ta'addan Boko Haram sun miƙa wuya

Tashar Channels tv ta ce wata sanarwa da babban jami’in yaɗa labarai na hedkwatar MNJTF, da ke Chadi ya fitar, ta naƙalto mai magana da yawun rundunar MNJTF, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi, ya bayyana hakan a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce sojojin ruwan Kamaru da na Nijar ne suka mika ƴan ta’addan bayan nasarar aikin da suka gudanar a yankin tafkin Chadi, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Daga cikin ƴan ta’addan da suka miƙa wuya akwai mayaƙa 14 da mata da ƙananan yara 55.

Ɗaya daga cikin mayakan ya miƙa wuya ɗauke da bindiga ƙirar AK-45 da kuma harsasai.

Yaushe ƴan ta'addan suka miƙa wuya?

Abubakar Abdullahi ya bayyana cewa ƴan ta'addan sun miƙa wuya ne a tsakanin ranakun 1 zuwa 6 na satan Yulin 2024.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bi dare sun sace 'yan jarida 2 tare da iyalansu a Arewa

"A ranar 6 ga watan Yulin 2024, aikin haɗin gwiwa tsakanin sojojin ruwan Kamaru da Nijar ya jawo ƴan ta'addan Boko Haram 56 sun miƙa wuya. Wannan adadin ya ƙunshi manyan maza mutum 13 da mata da ƙananan yara 43."
"Haka kuma a wannan ranar, an ceto iyalan ƴan ta'adda mutum 12 da suka haɗa da mata biyar da yara bakwai. An miƙa waɗanda suka miƙa wuya da waɗanda aka ceto ga dakarun Operation Hadin Kai, a Gamboru da Banki domin ɗaukar mataki na gaba."
"A ranar 1 ga watan Yulin 2024, dakarun sashe na huɗu a Jamhuriyar Nijar, sun karɓi Tijjani Muhammad mai shekara 24, wanda ya miƙa wuya ɗauke da bindiga ƙirar AK-47, jigida guda huɗu da harsasai masu yawa masu kaurin 7.62mm."

- Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi

Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana cewa dakarun sojojin Najeriya da ke gudanar da ayyukan cikin gida a faɗin ƙasar sun yi nasarar kashe ƴan ta'adda 135 a cikin mako guda.

Dakarun sojojin sun kuma cafke mutum 182 da ake zargi yayin da suka kuɓutar da mutum 140 da aka yi garkuwa da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng